Kalli hotunan dawowar Shugaba Buhari

A safiyar ranar Juma'a Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gida bayan shafe kwana 50 yana jinya a London. Ga hotunan yadda ya sauka a filin jiragin saman soji na Kaduna.

Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da ya sauka a Kaduna

Asalin hoton, Kaduna State Government

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma gida bayan shafe mako takwas yana jinya a birnin London na ƙasar Ingila.
Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da ya sauka a Kaduna

Asalin hoton, Kaduna State Government

Bayanan hoto, Shugaban ya sauka a wani filin jirgin sama na Kaduna saboda an rufe filin jirgin Abuja domin gyra shi
Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da ya sauka a Kaduna

Asalin hoton, Kaduna State Government

Bayanan hoto, Manyan jami'an gwamnatin jihar Kaduna da kuma na tarayya suka tarbe shi.
Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da ya sauka a Kaduna

Asalin hoton, Kaduna State Government

Bayanan hoto, Tuni shugaban ya tashi zuwa Abuja a wani karamin jirgin helikwafta
Shugaba Buhari da Archbishop na Canterbury Justin Welby

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Buhari lokacin da ya dauki hoto tare da Shugaban darikar Angalican Archbishop na Canterbury, Justin Welby, dab da zai bar London.
Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, An dade ana jiran dawowar Shugaba Buhari kuma tafiyar tasa ta jawo ce-ce-kuce a kasar
Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Nigerian Government

Bayanan hoto, Tuni shugaban ya isa Abuja kuma har ya gana da mataimakinsa da kuma wasu gwamnonin kasar