Ra'ayi Riga: Me ya sa yara a arewacin Najeriya suka fi kamuwa da tamowa?

Bayanan sautiLatsa alamar da ke sama domin sauraron cikakken rahoton
Ra'ayi Riga: Me ya sa yara a arewacin Najeriya suka fi kamuwa da tamowa?

Ƙungiyar Agaji ta Red Cross Society ta nuna damuwarta kan ƙaruwar ƙananan yara da suke kamuwa da tamowa a arewacin Najeriya, lamarin da ƙungiyar ta ce akwai tashin hankali.

Ƙungiyar ta ce lamarin ya fi ƙamari ne a jihohin da suke fama da matsalar tsaro, saboda matsalar tana hana mutane zuwa gonakinsu domin abincin da za su ci.

A rahoton ƙungiyar, an bayyana cewa fiye da yara miliyan biyar da dubu 400 ne suke fama da matsalar a jihohi tara da suke fuskantar rikice-rikice a rewacin Najeriya.

Jihohin da rahoton ya lissafa su ne Borno da Yobe da Kano da Katsina da Sokoto da Neja da Benue, inda rahoton ya ƙara da cewa lamarin ya shafi kashi 63 cikin 100 na ƙananan hukumomin jihohin.

Haka kuma alƙaluman sun nuna cewa kusan ƙananan yara miliyan biyu cikin adadin sun kamu da matsananciyar tamuwa, wadda a wasu lokuta ke kai wa ga mutuwa.

Shin shin yaya girman lamarin yake a jihohinku?

Wace barazana hakan ke yi?

Wane mataki ya kamata a ɗauka?

Wannan ne ya sa BBC ta gayyato masana da ƙwararru kan lamarin domin tattauna abubuwan da suke jawo hakan, da kuma bayar shawarwarin.