Amsoshin Takardunku 20/04/2025
Amsoshin Takardunku 20/04/2025
Yau ma kamar kowane mako cikin shirin namu na wannan mako - wanda Aisha Sharif Baffa ta gabatar - mun amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko mana.
Shin dole ne ƙasa sai ta tura jakada a kowace ƙasa ta duniya? Sannan me ke a ƙasa ta janye jakadanta daga wata ƙasar?
Ina tsirarun ƙabilu irin Margi da sauran ƙananan ƙabilu suka samo asalin tsagarsu ta gado?
Daga ƙarshe kuma mun byar da tarihin fitaccen ɗan gwagwarmayar nan na Jamhuriyar Nijar, Sadad Iliya Dan malam na NPSR, kamar yadda wani daga cikinku ya buƙata.