Kotu ta kori ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafen jam'iyyar APM a kan Tinubu

Nigeria Election

Asalin hoton, Court of appeal

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta kori ƙorafin jam'iyyar APM da ke neman a soke cancantar Bola Ahmed Tinubu, na jam'iyyar APC a zaɓen watan Fabrairu.

Mai shari'a Haruna Tsammani da ke jagorantar alƙalan kotun biyar, shi ne ya karanto hukuncin, lokacin da yake hukunci a kan ƙorafin jam'iyyar ta adawa.

Shi ne hukunci na farko a cikin hukunce-hukunce guda uku da kotun za ta yanke yayin zamanta na yau Laraba.

Jam'iyyar APM ta shigar ƙarar a kan Bola Ahmed Tinubu da Hukumar Zaɓe ta INEC da kuma Kabiru Masari, mutumin da ɗan takarar APC a wancan lokaci ya fara gabatar wa INEC a matsayin wanda ke mara masa baya kafin ya sauya shi da Kashim Shettima.

Jam'iyyar tana ƙalubalantar ɗaukar Kashim settima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa ne. Tana cewa maye shi a gurbin Kabiru Masari, ya saɓa wa tsarin mulki.

Mai shari'a Tsammani ya ce ƙarar da APM ta shigar, batu ne da ya shafi harkokin da ake la'akari da su kafin zaɓe, don haka kamata ya yi ta shigar da ƙarar a gaban babbar kotu.

Kotun dai ta ce ko kaɗan APM ba ta da hurumin na shiga cikin harkar da ta shafi jamiyyar da suka yi ƙara

Ko yadda suka gudanar da zaɓensu na cikin gida. Don haka ya yi watsi da ƙorafin, saboda ba su da hurumin a ciki.

Bayan dogon sharhi da kafa hujjojin shari'o'in da suka gabata, Mai shari'a Haruna Tsammani ya ce kotun ƙarar zaɓen, ta soke ƙarar da ke neman a soke cancantar Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Nigeria Election
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta fara zama don gabatar da hukunci a kan ƙorafe-ƙorafen da wasu 'yan takara suka shigar mata, bayan zaɓen watan Fabrairun 2023.

Jami'an tsaron da aka jibge tun da sanyin safiya, sun datse titin da ke zuwa harabar kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, inda ake zaman.

Kotun mai alƙali biyar a Abuja ta shafe watanni tana karɓar bahasi da kuma sauraron muhawara game da ƙorafe-ƙorafen maguɗi da jam'iyyun adawa na PDP da LP suka yi.

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaɓen Najeriya, inda ya samu yawan ƙuri'un da suka kai kashi 37 cikin 100 a zaɓen ranar 25 watan Fabrairu. Abin da ya ba shi galaba a kan Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na jam'iyyar LP.

Wannan, ba shi ne hukuncin ƙarshe da mai yiwuwa za a iya samu game da zaɓen ba, masana shari'a na cewa jam'iyyu na iya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli wadda za ta yanke hukunci na ƙarshe.

An ga manyan jami'an gwamnatin Najeriya ciki har da mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje da gwamnonin jam'iyyar, duk sun hallara a kotun.

Nigeria Election

Haka zalika, akwai wasu gwamnonin adawa kamar na jihar Bauchi, Bala Mohammed a kotun da shugaban PDP, Umar Iliya Damagum.

Sai dai ba a ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a harabar kotun ba,

Shi ma, Peter Obi na jam'iyyar Labour bai halarci zaman yanke hukuncin ba.