Gane Mini Hanya: Tare da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Tare da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

Gwamna Caleb Muftwang na jihar Filato ya ce suna aiki da mahukunta a Zariya don sanin abin da za su yi wa dangin matafiyan da aka kashe kwanan baya a jiharsa.

Ya ce tashe-tashen hankulan Filato na da alaƙa da gazawar hukumomi na hukunta masu haddasa rikice-rikicen da suka-ƙi-ci-suka-ƙi-cinyewa a jihar.

Gwamnan ya kuma ce rikice-rikicen masu nasaba da rashin yardar da ke tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, wanda kuma a wasu lokuta kan ritsa da matafiyan da ba su ji, ba su gani ba, ba lallai ne a iya kawo ƙarshensu cikin ƙanƙanin lokaci ba.

A zantawarsa da abokiyar aikinmu Aisha Shariff Bappa cikin filinmu na Gane Mini Hanya a wannan mako, Gwamna Muftwang ya fara da bayani kan rikice-rikicen da Filato ke yawan fama da su.