Ɗalibin Najeriya da ya shaida abin da ya faru a girgizar-ƙasar Turkiyya

Bayanan bidiyo, Latsa wannan hoto domin kallon bidiyo
Ɗalibin Najeriya da ya shaida abin da ya faru a girgizar-ƙasar Turkiyya

Ɗaliban Najeriya da ma na sauran ƙasashen Afirka da dama ne girgizar-ƙasa ta rutsa da su a Turkiyya.

Da dama daga cikin su sun nemi mafaka a wuraren da gwamnati ta tanada kafin al'amura su lafa.

Shafi'u Jibril shi ne shugaban ɗaliban Afirka a birnin Gaziantep na ƙasar Turkiyya, ya shaida wa BBC yadda rayuwa ta kasance bayan faruwar girgizar-ƙasar.