Ra'ayi Riga: Kan yawaitar mutuwar mata a wurin haihuwa 29/03/2025
Ra'ayi Riga: Kan yawaitar mutuwar mata a wurin haihuwa 29/03/2025
A shirinmu na Ra'ayi Riga wannan makon, mun nazari ne kan batun yawaitar mutuwar mata a wurin haihuwa wanda muka naɗa a birnin Kano.
Bincikne nigerian health watch mai bibiyar al'amura a kan harkokin lafiya a Najeriya ta yi, ta gano cewa yankin arewaci maso gabashin Najeriya ne ya fi fama da wannan matsalar, sannan Kano ce kan gaba a cikin jihohi.
Shin me yake jawo mutuwar mata wajen haihuwa?
Me ya sa Kano ta kai wannan mataki?
Me ya kamata a yi?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna a cikin shirin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.