Ra'ayi Riga: Kan ƙarin kuɗin kira da na data a Najeriya 14/02/2025
Ra'ayi Riga: Kan ƙarin kuɗin kira da na data a Najeriya 14/02/2025
A wannan makon ne 'yan Najeriya suka wayi gari kwatsam da ganin ƙarin kuɗin kiran waya da na data da kamfanonin sadarwa suka yi.
Hakan na zuwa ne bayan amincewar da hukumomin Najeriyar suka yi kan buƙatar da kamfanonin sadarwar suka gabatar na neman izinin ƙarin kuɗin bisa dalilai na tsadar gudanar da ayyukansu.
Wannan ƙari ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan ƙasar ganin yadda daman suke ƙorafi da rashin ingantaccen sabis daga kamfanonin sadarwar.
Shin nawa ne ƙarin da kamfanonin suka yi?
Wane tasiri ƙarin zai yi a rayuwarku?
Wane mataki hukumomi ke ɗauka kan lamarin, ko kuwa shikenan ruwa ta sha?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna a cikin shirin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.