Gane Mini Hanya: Tare da gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya 10/05/2025

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Tare da gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya 10/05/2025

Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ya ce halayyar wasu ƴan ƙasar na yin abin da suka ga dama a fannoni daban-daban shi ne babban abin da ya janyo koma-baya a ƙasar.

Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya ce wannan dalilin ya sa ake jin jiki yayin da shugaba Tinubu ke ɗaukar matakan gyara tattalin arziki da sauran fannoni.

A cikin wannan wata ne gwamnan zai cika shekara biyu a zango na biyu na shugabancin jihar, kuma a filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon, Zahraddeen Lawan ya fara da tambayarsa ko kawo yanzu ya cimma alkawuran da ya ɗauka wa Gombawa?