Yankunan da Amurka ta saya ta kuma haɗe da ƙasarta

Tutar Amurka

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Guillermo D. Olmo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
  • Lokacin karatu: Minti 5

A daidai lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump ke cigaba da yunƙurin mallakar yankin Greenland - hankali ya fara komawa kan yadda zai karɓi yankin daga Denmark.

Trump ya nanata buƙatar mallakar Greenlad saboda tsaro.

Sannan a wasu lokutan baya ya bayyana cewa zai iya amfani da ƙarfin tsiya wajen mallakar yankin, duk da cewa a yanzu ya ce zai fi mayar da hankali wajen sasanci da sulhu maimakon amfani da ƙarfi.

Wannan ya sa muka yi nazari tare da tattara wasu yankuna da Amurka ta saya a baya domin assasa ƙasar ta yanzu.

Wasu yankuna

Louisiana (1803)

Shugaban Amurka Thomas Jefferson ne ya yanke shawarar sayen yankin Louisiana daga Faransa a shekarar 1803.

Yanki ne mai girman murabba'in faɗin kilomita 2,000,000, wanda hakan ya sa mallakarsa ya ƙarfafa ƙasar.

Shugaban Faransa na wancan lokacin, Napoleon Bonaparte ne ya sayar wa Amurka da yankin bayan zanga-zanga da rashin amincewa da safarar bayi ta cikin Saint Domingue (wato Haiti a yanzu), da barazanar yaƙi daga Birtaniya.

Amurka ta saya yankin ne daga Faransa a wata yarjejeniya da aka shiga a watan Nuwamban 1803 a kan kuɗi $15m, wanda a yanzu yake daidai da dala miliyan 400 a yanzu.

Sayen Louisiana daga Faransa ne farkon babban yunƙurin faɗaɗa ƙasar Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sayen Louisiana daga Faransa ne farkon babban yunƙurin faɗaɗa ƙasar Amurka

Mexican Cession (1848)

A tsakankanin shekarun 1840s ne Amurka suka yi amannar cewa akwai buƙatar faɗaɗa ƙasar ta yankin tekun Pacific ta yankin Mexico.

Zanen da ke nuna yunƙurin faɗaɗar Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanen da ke nuna yunƙurin faɗaɗar Amurka

Daga cikin waɗanda suka fi sha'awar faɗaɗa Amurka akwai Shugaba James K Polk, wanda bayan an rantsar da shi a 1845, ya gaji rikicin mallakar Texas, bayan ta samu ƴanci daga Mexico a 1836.

Amurka ta mamaye Texas ne a 1845 ta zama jiha a Amurka, sannan bayan shekara ɗaya yaƙi ya ɓarke tsakanin sojojin Amurka da na Mexico, inda har majalisar Amurka ta amince a ƙaddamar da yaƙi a Mexico.

Wani masanin tarihi Jay Sexton ya ce a lokacin Amurka ta nuna sha'awar mallakar California, wadda ita ma a lokacin tana ƙarƙashin Mexico.

Nasarar da Amurka ta samu a yaƙin da Mexico ne ya sa a 1848 ta faɗaɗa ƙasar ta kudanci.

Nasarar da Amurka ta samu a yaƙin da Mexico ne ya sa a 1848 ta faɗaɗa ƙasar ta kudanci.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nasarar da Amurka ta samu a yaƙin da Mexico ne ya sa a 1848 ta faɗaɗa ƙasar ta kudanci.

Amma daga baya Amurka ta biya dala miliyan 15, daidai da kusan dala miliyan 615 ta yanzu domin mallakar yankin a hukumance, sannan ta ƙara da California da Nevada da Utah da wasu yankunan Arizona da Colorado da New Mexico da Wyoming na yanzu.

Amurka ta ƙara da kusan faɗin ƙasan kilomita 1,360,000 daga Mexico.

La Mesilla (1853)

Bayan yaƙin Amurka da Mexico a 1848, an cigaba da samun takun-saƙa a tsakanin ƙasashen biyu.

Hakan ya sa aka shiga wata yarjejeniya a 1854 domin sayar da wani yankin na Mexico da ya koma cikin yankin Arizona da New Mexico.

Ana kiran yankin da Venta de la Mesilla ne a Mexico, ko kuma Gadsden a Amurka, kuma Washington ta kashe kusan dala miliyan 10 na wancan lokacin, wanda yake daidai da dala miliyan 421 a yanzu.

Alaska daga Rasha (1867)

A shekarar 1867 ne sakataren harkokin wajen Amurka, William Seward ya nace wajen sayen Alaska daga Rasha.

A lokacin Amurka ta ce tana matuƙar buƙatar yankin, a yayin da a ɗaya ɓangaren kuma Rasha take ganin ba ta wani buƙatar yankin sosai.

Salon mallakar Alaska ne Trump yake yunƙurin amfani da shi wajen mallakar Greenland

Asalin hoton, Al Drago / Getty

Bayanan hoto, Salon mallakar Alaska ne Trump yake yunƙurin amfani da shi wajen mallakar Greenland

Seward ya sayi yankin ne mai faɗin kilomita 1,554,000 daga Rasha a kan dala miliyan 7.2, kimanin dala miliyan 158 a yanzu, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a Amurka, inda wasu ke ganin an kashe kuɗi da yawa.

Yunƙurin sayen Alaska daga Rasha ya haifar da ce-ce-kuce

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yunƙurin sayen Alaska daga Rasha ya haifar da ce-ce-kuce

US Virgin Islands daga Denmark (1917)

Lokaci na ƙarshe da Amurka ta saya wani yanki shi ne wanda ta mallaki yankin na Denmark, wanda shi ma sakataren harkokin wajen ƙasar na wancan lokacin, William Seward ya jagoranta.

Ƴan Greenlander dai sun yi zanga-zangar kan yunƙurin

Asalin hoton, Sean Gallup/Getty

Bayanan hoto, Ƴan Greenlander dai sun yi zanga-zangar kan yunƙurin

Gaɓar ta Saint Thomas na cikin tsibirai guda uku da suka haɗa tsibirin Virgin Island na yanzu da Amurka ta saya daga Denmark.

A 1867 ne ƙasashen biyu suka cimma yarjejeniyar sayar da yankin a kan dala miliyan 7.5, kusan dala miliyan 164 a yanzu, amma majalisar Amurka ta ƙi amincewa.

Denmark ce ta amince ta sayar da yankin ga Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Denmark ce ta amince ta sayar da yankin ga Amurka

Ɓarkewar yaƙin duniya na farko da barazanar sojojin ruwan Jamus kan jiragen ruwan Amurka ne suka ƙara jan hankalin Amurka, inda Washington ta fara fargabar Jamus na iya kai farmaki a Denmark ta mallaki tsibirin.

Shugaban Amurka na lokacin ne ya umarci sakataren harkokinsa ya yi gargaɗi ga Denmark, inda ya ce matuƙar ƙasar ta ƙi sayarwa, Amurka za ta ƙwace da ƙrfi.

Astrid Andersen, wani babban mai bincike a cibiyar nazarin harkokin ƙasashen waje ta Danish Institute for International Studies, ya ce akwai wahalar fahimtar alaƙar da ke tsakanin abin da ya faru da tsibirin US Virgin Islands da abin da ke faruwa.

"Abin da muke gani a game da Greenlad a yanzu shi ne Amurka ta ce mana ne: 'ko dai ku sayar mana ko mu ƙwace," in ji Andersen.