Hikayata 2023: Labarin RINA A KABA

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron labarin RINA A KABA
Hikayata 2023: Labarin RINA A KABA

RINA A KABA, labari ne da aka gina a kan wata matar auren da ta ɗauki cushe-cushe da shaye-shayen magungunan mata barkatai a matsayin babban jigo a zamantakewar aure a ƙoƙarinta na ganin ta turbuɗe hasken tauraruwar kishiyarta.

Shi ne labarin da ya zamo na ɗaya a gasar BBC ta Hikayata, 2023.

Sai dai garin neman gira ta rasa idanuwanta gaba ɗaya, domin ta haɗu da illoli da dama da suka tarwatsa lafiyarta daga ƙarshe ta tsinci Talatarta a Laraba.

An haifi marubuciyar, Aisha Adam Hussain mai shekaru 27 a unguwar PRP, ƙaramar hukumar Nassarawa da ke jihar Kano.

Aisha tana da aure da yara biyu. Ta yi karatunta daga firamare zuwa matakin NCE a Kano. Yanzu haka Aisha na cigaba da karatun digiri a kwalejin horar da malamai ta FCE da ke Kano.