Gane Mini Hanya: Kan muhimmancin radiyo 15/02/2025

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Kan muhimmancin radiyo 15/02/2025

A wannan makon ne aka yi bikin Ranar Radiyo ta Duniya.

Hukumar Raya Ilmi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ce ta keɓe kowace ranar 13 ga watan Febrairu, a matsayin Ranar Radiyo domin jan hankalin duniya kan rawar da radiyo ke takawa wajen cigaban al'umma ta fuskoki daban-daban.

Sai dai wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin radiyo na fuskantar ƙalubale na ja-da-baya da farin jininsa ke keyi sakamakon ɓullar kafofin sada zumunta na zamani.

Kan haka ne a filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon Haruna Shehu Tangaza ya tattauna da 'yan wata babbar ƙungiyar masu sauraren radiyo a Najeriya kan tasirin da radiyo ke da da kuma ƙalubalan da yake fuskanta.