Wace riba ƙasashen Afirka za su samu a dangantakarsu da Amurka?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Damian Zane
- Lokacin karatu: Minti 5
Shugabannin Afirka na taruwa a Addis Ababa, babban birnin Habasha domin gudanar da taron da aka saba yi duk shekara a karshen makon nan, a daidai lokacin da gurbin nahiyar a duniya ke cikin wani sauye-sauye.
Da yake magana a birnin Davos a watan da ya gabata, Firaministan Canada Mark Carney, ya bayyana yadda makomar ƙasashe da kuma dangantaka take: inda ya ce yawancin kasashe na son a dama da su.
Ga shugabannin Afirka, waɗanda suka ɗauki shekaru da yawa suna jayayya cewa a tafi da su a harkoki, hakan ba wani sabon abu bane.
Sai dai a wa'adinsa na biyu, shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara haɓaka yadda manyan kasashen duniya suka mamaye harkokin duniya da kuma kawar da ra'ayin bangarori daban-daban.
Sabon tsarin tsaro na fadar White House, ya ce ba za a mayar da hankali iri ɗaya ga kowane yanki a duniya ba. Yayin da Trump ke ci gaba da gudanar da harkokinsa da kuma irin lokaci da ya shafe a Gabas ta Tsakiya, alamu sun nuna cewa ba zai mayar da hankali kan Afirka ba yadda ya kamata.
Ƙasashe marasa galihu waɗanda yawanci suka dogara kan irin tallafin da suke samu daga hukumomi irinsu Majalisar Ɗinkin Duniya, Bankin Duniya da kuma Cbiyar Cinikayya ta Duniya, ya zama tilas yanzu su sake duba yanayin dangantaka.
Waɗannan matakai sun janyo ana aza ayar tambaya cewa ta yaya nahiyar za kai wajen da sauran nahiyoyi suke a duniya.
Masana sun bayyana cewa akwai barazanar cewa za a iya barin ƙasashen Afrika a baya muddin ba su samar da wani tsari na bai-ɗaya ba.
Sai dai nahiyar na da ɗimbin albarkatun ƙasa da za su iya janyo ra'ayion manyan ƙasashe a duniya.

Asalin hoton, EPA
A tsawon shekaru uku da suka wuce, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya faɗa wa shugabannin nahiyar a wani taro a Amurka cewa, "Amurka za ta tsaya wajen ganin nahiyar Afirka ta samu makoma mai kyau".
Wannan ya biyo wani daftari da fadar White House ta fitar kan yankin kudu da hamadar Sahara na Afirka, inda ta kwatanta yankin a matsayin "mai muhimmanci wajen ci gaban muradun mu".
Sai dai masu suka sun aza ayar tambayar cewa ko da gaske fadar White House ɗin take kan haka, ganin cewa a ƙasashen Cape Verde da Angola ne kaɗai shugaba Biden ya kai ziyara daf kafin ya sauka.
Shi ma tun zuwansa kan mulki, shugaba Trump ya bayyana cewa komai zai yi Amurka ce a farko.
"Ba za mu iya mayar da hankali iri ɗaya ga kowane yanki ba da kuma matsalolinsu a duniya," kamar yadda tsarin tsaron White House ya bayyana a watan Nuwambar da ta wuce.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Akwai wasu yarjejeniyoyi da a Amurka ta kulla da da Kongo kan albarkatun ƙasa a watan Disamba, wanda ya zo daidai lokacin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rwanda.
An yi haka ne da zimmar samar da hanyoyi masu ɗorewa na kai kayaki masu muhimmanci zuwa Amurka, a gefe guda kuma da ƙarfafa zuba jari a Jamhuriyar Kongo mai ɗimbin albarkatu na haɗa abubuwan lantarki.
Wani ƙwararre kan harkokin nahiyar Afirka a Jami'ar Georgetown, Ken Opalo, ya nuna damuwar cewa tsarin hulɗar kasuwanci tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka na nufin cewa matsayin ciniki ga kasashen zai yi rauni matuka, saboda haka ba za a iya samun yarjejeniyoyi masu inganci ba.
Ya faɗa wa BBC cewa "idan za a ɗau misali da Kongo, za a ga cewa Amurka ta mayar da hankali ne kan albarkatun ƙasar don ganin kamfanonin ƙasar sun samu ƴancin haƙar ma'adinai a can da kuma haɓaka tattalin arzikinsu, wanda ba shi yankin ke buƙata ba.
"Yankin na son samun ƙarin dama ta shiga kasuwanni, zuba jari da kuma janyo hankalin Amurka ga sauran fannoni ba wai ma'adinai kaɗai ba."
Ministan harkokin ma'adinai na Kongo ya yi watsi da batutuwan. Da yake magana a wani taro kan harkokin ma'adinai a birnin Cape Town a makon nan, Louis Watum Kabamba, ya ce ƙasarsa "ba a kyauta ƙasarsa za ta sayarwa Amurka abubuwa ba".
Ba Amurka ce kaɗai ke da iko ba. China ta zarta Amurka a wajen zuba jari a Afrika a tsawon gomman shekaru, duk da cewa matsayin ya sauya a shekarar da ta gabata.
Wasu ƙasashe kamar Rasha, Turkiyya da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa su ma suna cimma yarjejeniyoyin zuba jari da kuma na tsaro a nahiyar ta Afirka.
A ɓangaren tsaro, gaza kawo karshen yaƙin basasar Sudan ya janyo MDD cewa rikicin shi ne rikicin jin-ƙai mafi muni a duniya.
An zargi Turkiyya da samarwa sojojin Sudan makamai duk da nuna cewa ita ƴar ba-ruwana ce. Iran da Rasha ma na fuskantar irin wannan zargi. Sai dai duka sun musanta, amma a watan Fabrairun bara Rasha ta cimma yarjejeniya da gwamnatin mulkin sojin Sudan don kafa sansanin soji ruwa a ƙasar.
A ɗaya ɓangare, an zargi UAE da mara wa dakarun RSF baya, sai dai ta musanta batun.
"Rashin kawo karshen yakin Sudan na ɗaya daga cikin matsaloli na haɗin-kai da nahiyar ke da shi.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Ghana John Mahama, na son kawar da irin wannan shakku.
Mahama, kamar Carney, ya yi jawabi a birnin Davos.
Ya ce raguwar tallafi da kuma cigaba, ya janyo duniya na kan hanyar rugujewa.
''Dole ne Afrika ta tsamo kanta da kanta," in ji shi
Ya ce nahiyar ta rasa ƴancin kanta kuma ta faɗa yanayin dogaro da wasu. Wannan kuma gaskiya idan aka duba ɓangaren ba da agaji - musamman na lafiya da kuma ilimi - har ma da tsaro, in ji shi, inda ya ƙara da cewa idan aka zo ga batun albarkatun ƙasa, "Mu ke samar da albarkatu masu muhimmanci ga duniya amma ba mu cin ribarsa."
Shugaban na Ghana na da'awar ganin an ƙara zuba jari a fannoni masu muhimmanci a nahiyar ta hanyar shirinsa na sake gyara Ghana.
Sai dai an sha jin irin waɗannan kiraye-kiraye a baya kuma tambayar ita ce ko akwai damar cewa yanzu abubuwa za su sauya.











