Ra'ayi Riga: Kan bukukuwan babban sallah
Ra'ayi Riga: Kan bukukuwan babban sallah
Al'ummar Musulmi a ƙasashen duniya na ci gaba da shagulgulan Idin Babbar Sallah yayin da ake kokawa da tsadar farashi da matsin rayuwa.
Bana mutane sun yi ta nuna damuwa a kan tsadar raguna a Nijeriya, yayin da a ƙasashe kamar Nijar duk da 'yan kasuwa na cewa farashin ragunan ya karye, amma da yawa ba su iya yin layya ba.
Haka kuma, an koka da tsadar musamman kayan miya, kamar tumatur da attaruhu da citta, waɗanda suka yi tashin gwauron zabi.
Mutane da yawa dai na bayyana farin cikin cewa, ko ba komai dai sun yi sallah lafiya.
A jawabansu na Barka da Sallah, shugabannin siyasa da sarakuna sun yi ta nanata buƙatar yin addu'o'in neman zaman lafiya da ingantuwar tsaro da sauƙi kan tsadar rayuwar da ake fama da ita.