Ra'ayi Riga: Kan gallaza wa ƙananan yara 18/04/2025

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Ra'ayi Riga: Kan gallaza wa ƙananan yara 18/04/2025

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan ƙaruwar gallaza wa ƙananan yara da a wasu lokuta kan kai ga yi wa yaro mummunan rauni ko nakasa ta har abada ko ma kisa.

A Najeriya ana samun ƙaruwar rahotannin gallaza wa ƙananan yara a cikin jihohi da dama na ƙasara.

Alƙaluma daga hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Najeriya sun nuna cewa a watan Maris, musguna wa yara ta hanyar yin watsi da su, na cikin manyan laifukan take haƙƙin bil'adama da aka aikata a ƙasar.

Shin me yake janyo ƙaruwar waɗannan al'amura na gallazawa yara a Najeriya? Me hukumomi ke yi kan waɗannan abubuwa na tayar da hankali kuma ta yaya za a shawo kansu?

Wasu daga cikin batutuwan da shirin ya tattauana kenan