Dabarun yin bacci cikin minti biyu, ko kuna aiki

Akwai wani tsari na sojoji da ake fara bacci a minti biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai wani tsari na sojoji da ake fara bacci a minti biyu
    • Marubuci, Kate Bowie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kowa na so ya ga ya fara bacci cikin sauri da sauƙi da zarar lokacin da yake so ya fara baccin ya yi, amma miliyoyin mutane suna fama da cutar rashin bacci da ake kira 'insomnia' ko kuma suke fama da wahalar fara bacci.

Yanayin yadda mutane suke fama da matsalar ya bambanta, amma bincike ya nuna cewa tsakanin kashi 5 zuwa kashi 50 na mutanen duniya suna fama da cutar.

Yanayin rashin baccin ne ya sa mutane da dama suke neman hanyoyin da za su riƙa domin fara bacci cikin sauƙi, ciki har da "baccin sojoji" da aka ce za a iya yin bacci a cikin minti biyu.

Tsarin dai ya samu karɓuwa a kafofin sadarwa ta TikTok, inda bidiyoyin ke samun miliyoyin masu kallo, inda suke fara bacci da zarar sun bi tsarin.

Amma masana sun yi gargaɗin cewa amfani da tsarin zai iya jawo tsaiko wajen fara baccin saboda "sa rai".

Mene ne tsarin baccin sojoji?

Wani mai horas da Amurkawa gudun fanfalaƙi mai suna Lloyd "Bud" Winter ne ya fara bayyana tsarin a 1981 a littafinsa mai suna "Relad and Win."

A lokacin Yaƙin Duniya na biyu ne Winter ya fito da tsarin domin sojojin ruwan Amurka su samu damar runtsawa, su tashi su ci gaba da aiki ba tare da matsala ba. Littafin ya bayyana tsare-tsaren:

  • Ka kwantar da kanka, ka saki haɓarka da fuska, sai ka yi numfashi.
  • Ka saki kafaɗunka su baje, sannan ka sake numfasawa, sai ka saki ƙirjinka.
  • Ka saki hannayenka a kan kujera ko gado ka shimfiɗa damtsenka a gefe ɗaya, sai ka juya ɗaya gefen.
  • Ka miƙa ƙafarka a hankali a hankali. Ƙafa ɗaya bayan ɗaya.
  • Ka warware zuciyarka, sannan ka kwatanta kanka kana kwance kana bacci a wani waje mai kyau.
  • Idan da hali, ka daina tunanin komai.
  • Winter ya yi iƙirari cewa atisayen nan a mako shida zai sa mutum ya saba da yadda zai yi bacci a minti biyu a duk lokacin da suke son fara bacci.

'Zai saka mutum damuwa'

Amma masana sun ce tunanin fara bacci cikin sauri zai iya jefa mutum cikin damuwa.

"Tunanin fara bacci da sauri da kuma amfani da wannan tsarin domin fara bacci cikin minti biyu yana da illa," in ji wani masanin ƙwaƙwalwa mai aiki da sojoji, Dr Allison Brager says.

A ƙa'ida ana buƙatar tsakanin minti biyar zuwa 20 domin fara bacci, don haka yunƙurin fara bacci a cikin minti biyu zai iya rage baccin.

"Kawai za ka shiga damuwa ne a ƙoƙarinka na fara bacci a lokacin da a maganar gaskiya ba zai yiwu ba," in ji ta.

Idan ka fara bacci a cikin minti biyu, akwai alamar kana ɗauke da wasu cututtuka ne kamar ta rashin bacci.

Brager ta ce ta san sojojin da suke amfani da tsarin, amma ta ƙara da cewa yanayin wahalar da sojoji suke yi, ba abin mamaki ba ne don bacci ya kwashe soja a cikin minti biyu.

Yaya zan fara bacci da sauri?

Mutanen da suke fama da rashin bacci za su fi fuskantar matsala idan sun yi amfani da tsarin baccin na minti biyu, in ji Dr Hugh Selsick.

"Yawanci mutanen da na duba, sun faɗa min cewa sun yi amfani da tsarin amma bai musu aiki ba," in ji shi.

An daɗe ana cewa baccin awa 8 ake buƙata domin samun lafiya, amma shi ma wannan na ƙara jefa mutane cikin damuwa.

Ya ƙara da cewa yanayin baccin da mutum ke buƙata ya danganta da yanayin mutum da ma gado.

Selsick ya kwatanta da girman takalmi, inda ya ce kowa na da lambar takalmin da yake sakawa.

"Kawai abin da ake buƙata shi ne mutum ya yi baccin da kake tunanin kana buƙata," in ji shi.

Amma duk da haka, idan kana so ka riƙa yin bacci da sauri, ga wasu matakai guda uku:

  • Tsara lokaci: Idan kana kwanta a lokaci iri ɗaya, hakan zai taimaka da zarar lokacin ya yi ka fara jin bacci, haka ma tashi daga baccin.
  • Baccin rana: Idan ka guji baccin, baccin zai taru, da zarar lokacin baccin ya yi zai zo.
  • Zuwa bacci: Masanin ya ce mutum ya guji zuwa bacci idan ba ya jin bacci.
Ana shawartar sojoji su riƙa ɗan rage baccin rana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana shawartar sojoji su riƙa ɗan rage baccin rana

Abin da za mu koya daga baccin sojoji

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsarin baccin sojoji na minti biyu ba daidai ba ne, in ji Dr Alex Raecliffe, masanin harkokin bacci a rundunar sojin Birtaniya.

Sai dai ya ce ba komai ba ne ba daidai a game da tsarin, inda ya ce ana koyar da sojoji miƙa da numfashi a atisaye.

Sojojin da suke bakin daga ma ana shawartar su da su riƙa baccin rana kaɗan kaɗan a duk lokacin da suka samu dama, saboda sun san zai yi wahala su samu cikakken bacci a dare.

Sai dai ba a cika shawartar waɗanda suke so su yi bacci da sauri su riƙa baccin rana ba, mutane kamar masu shayarwa, waɗanda suke shan wahala wajen baccin dare, za su iya amfani da raba wajen rage bacci.

Haka kuma Brager ta ce akwai wasu dabaru bacci da ya kamata fararen hula su koya daga sojoji.

Idan ka tsara wa ƙwaƙwalwarka lokacin bacci, lokacin na yi za ka fara jin bacci.

"Ya danganci yanayin abin da ka tsara, da kuma yadda kake amfani da shi sau da ƙafa," in ji ta.

Kwantawa a cikin lokaci da kashe waya da karanta littafi da kashe dabaru ne masu kyau.

"Jikin zai saba da tsarin da ka ɗaura shi ne, don haka idan ka fara, sai ka ci gaba da yi, a hankali jikinka zai saba fara bacci a lokacin da kake so," in ji Brager.