Ra'ayi Riga kan matsalar lantarki a arewacin Najeriya 02/11/2024

Bayanan sautiLatsa hoton sama domin sauraro
Ra'ayi Riga kan matsalar lantarki a arewacin Najeriya 02/11/2024

A Najeriya musamman jama'ar arewacin ƙasar na ci gaba da duba asarar da suka tafka sakamakon katsewar wutar lantarki a arewacin ƙasar kusan tsawon mako biyu, al'amarin da ya jefa yankin cikin duhu.

Duk da cewa an gyara wutar a wasu sassan jihohin arewar amma kawo yanzu Jami'an hukumar rarraba wutar lantarkin na cewa suna ƙoƙarin dawo da lantarkin a sauran wurare.

Mahukuntan ƙasar sun ɗora alhakin katsewar lantarkin a kan masu satar kayan lantarki da kuma 'yan bindiga da suka lalata babban layin lantarkin Shiroro zuwa Kaduna.

A wannan shiri mun tattauna kan yadda matsalar ta shafi al'ummar arewacin Najeriyar wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.