Ra'ayi Riga: Kan yawaitar tare matafiya ana musu kisar gilla a Najeriya
Ra'ayi Riga: Kan yawaitar tare matafiya ana musu kisar gilla a Najeriya
Da alama dai har yanzu tsugunu ba tare ƙare ba kan tare mafiya a hanyoyin Najeriya ana musu kisar gilla, lamarin da kan jefa mutane da dama cikin fargaba, musamman idan za su yi tafiya zuwa wasu jihohin ƙasar.
A kwanakin baya-bayan nan an samu labarin tare matafiya ƴan ɗaurin aure da aka tare, aka kashe a jihar Filato, sannan aka sake jin labarin aukuwar lamarin a jihar Benue.
Sai dai an daɗe ana samun irin waɗannan matsalolin na tare matafiya a kashe.
To shin ko yaya girman wannan matsala ta kai?
Me ya janyo yawaitar matsalar a Nijeriya?
Kuma me ya kamata a yi don magance matsalar?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirinmu na ra'ayi riga na wannan makon ya tattauna a kai.