Gane Mini Hanya: Kan Ranar Ruwa ta Duniya
Gane Mini Hanya: Kan Ranar Ruwa ta Duniya
To yau ce Ranar Ruwa ta Duniya. An dai ware ran 22 ga watan Maris ta kowacce shekara don yi bikin ranar da nufin wayar da kan al'umma game da muhimmancin tsaftataccen ruwan sha.
Kan haka ne wakilinmu, Zahraddeen Lawan ya ziyarci wani ƙauye a jihar Jigawa wanda a shekarun baya ya yi fama da rashin ruwa, amma sanadiyar shirin BBC Hausa, gwamnati ta gina musu sabuwar cibiyar samar da ruwa, kuma ya shiga garin na gware don ganin yadda rayuwarsu ta sauya.