Wasannin neman shiga gasar nahiyar Afrika da za su fi zafi

Asalin hoton, Getty Images
Da alama gwarzuwar gasar nahiyar Afrika Ivory Coast za ta iya kai wa ga gasar ta 2025 da za a yi a Morocco, amma da alama Najerioya ta fada wani rukuni mai matukar rintsi.
Raba rukunin da aka yi a birnin Johannesburg, Super Eagles ta tsinci kanta cikin rukuni daya da Benin, Rwanda da kuma Libya.
Yanzu tsohon kocin Najeriya Gernot Rohr ne ke horar da Benin, kuma ya doke Najeriya da ci 2-1 a wtan jiya a wasannin share fagen shiga gasar kofin duniya ta 2026.
Najeriya yanzu na neman sabon koci biyo bayan ajiye aikin da Finidi George ya yi wanda ya koma Rivers United - sai dai har yanzu hukumar kwallon kafa ta ƙasar ba ta tabbatar da tafiyarsa ba a hukumance.
Ivory Coast da ta lashe gasar nahiyar karo na uku bayan doke Najeriya a wasan ƙarshe a watan Fabirairu, za ta fafata da gwarzuwar gasar 2012 Zambia, Sierra Leone da kuma Chadi.
Kocin tawagar Elephants Emerse Fae ya taimaka wajen raba rukunin da aka yi a Johannesburg kuma ya yi farin ciki da sakamakon.
"Mun yi wasa da Zambia a wasan share fagen Afcon na baya, dan haka mun san tawagarsu sosai da sosai," in ji Fae.
"Abu mafi dadi a gare ni shi ne, tafiyar da za mu yi ba doguwa ba ce. Don haka abin zai mana dadi."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tawagar kasashe 48 ɗin an raba su zuwa rukunai 12 ne zuwa kuma gida hudu, yayin da tawagogi biyu na kowanne rukuni za su samu zuwa Morocco a ƙarshe.
Masu masaukin baƙi na da kujerar dindindin a gasar, don haka tawaga ɗaya ake nema a rukunin da suke, wanda ya hada da Gabon, Central African Republic da kuma Lesotho.
Za a yi wasanni shida ne na neman gurbin a watan Satumba da Oktoba da kuma watan Nuwambar wannan shekarar.
Za a fara wasan Afcon 2025 a ranar 21 ga watan Disambar shekara mai zuwa, a kuma yi wasan karshe na gasar a ranar 18 ga watan Janairun 2026.
Gasar za buga ta ne lokacin da ake wasannin Premier Ingila na ƙarshen shekara da kuma gasar Uefa Champions Lig ta Turai.
Wannan ne karon farko da ake buga gasar a watan Nuwamba a tarihi, kuma zai shiga lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara.
Rukunan samun shiga Afcon 2025
Rukunin A: Tunisia, Madagascar, Comoros, The Gambia.
Rukinin B: Morocco, Gabon, Central African Republic, Lesotho.
Rukinin C: Egypt, Cape Verde, Mauritania, Botswana.
Rukinin D: Nigeria, Benin, Libya, Rwanda.
Rukinin E: Algeria, Equatorial Guinea, Togo, Liberia.
Rukinin F: Ghana, Angola, Sudan, Niger.
Rukinin G: Ivory Coast, Zambia, Sierra Leone, Chad.
Rukinin H: DR Congo, Guinea, Tanzania, Ethiopia.
Rukinin I: Mali, Mozambique, Guinea-Bissau, Eswatini.
Rukinin J: Cameroon, Namibia, Kenya, Zimbabwe.
Rukinin K: South Africa, Uganda, Congo, South Sudan.
Rukinin L: Senegal, Burkina Faso, Malawi, Burundi.











