Lafiya Zinariya: Hatsarin kamuwa da cutar ƙanwar ƙyanda ga mai ciki

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron shirin
Lafiya Zinariya: Hatsarin kamuwa da cutar ƙanwar ƙyanda ga mai ciki

Mace mai juna biyu, musamman mai ƙaramin cikin da ta kamu da cutar ƙanwar ƙyanda 'Rubella' kan haifi jariri da nakasa ko wasu manyan matsaloli na kiwon lafiya.

Wasu daga cikin matsalolin da za su iya shafar jaririn sun haɗa samun huji a zuciya, ko ya zo da buɗaɗɗen baya, makanta, kurumta, ɗan ƙaramin kai da matsalar da ta shafi ƙwaƙwalwa.

Sai dai akwai riga-kafin wannan cuta, wanda tuni wasu ƙasashe na amfani da shi wurin kawar da cutar a tsakanin al'umma.

Hukumomi a Najeriya na shirin sanya wannan riga-kafi, cikin jerin riga-kafin da ake yi wa yara don kare su daga wannan cuta.

Ƙasar na daga cikin ƙasashen duniya da ke fuskantar annobar ƙyanda lokaci zuwa lokaci, cutar da ke da kamanceceniya da ƙanwar ƙyanda wurin alamominsu.

Lamarin da ke sanadiyyar mutuwar ƙananan yara masu yawa.