Lafiya Zinariya: Shin kin san matsalolin da ke biyo ɗaukewar jinin haila?

Bayanan sauti
Lafiya Zinariya: Shin kin san matsalolin da ke biyo ɗaukewar jinin haila?

Kamar yadda ake samun yara mata da ke fara jinin haila a kullum, haka ake samun matan da ke dainawa a fadin duniya.

Ɗaukewar jinin al'ada shi ne matakin girma ga mata a rayuwa, kuma wani muhimmin lokaci ne da ya kamata mace ta san irin sauye-sauyen da ke faruwa da ita.

Haka kuma yana da muhimmanci mace ta san irin matakan da ya kamata ta ɗauka domin kasancewa cikin koshin lafiya.

Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa matar da ta shafe watanni 12 a jere ba ta ga jinin al'ada ba, ta daina jinin al'ada ke nan.

Haka zalika, ɗaukewar jinin na nufin baza ta ƙara ɗaukar ciki ba, domin ta daina haihuwa.

Domin jin cikakken bayani kan abubuwan da ke biyo bayan ɗaukewar jinin al'ada a rayuwar mace, latsa makunnin da ke sama.

Ƙwararriyar likitar mata, Farfesa Yamuna Aminu Ƙani ta yi dogon bayani kan wannan batu.