Hikayata: Labarin Tsaiwar Wata
A ci gaba da kawo muku labarai 12 da alƙalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo, a yau za mu kawo muku labarin Tsaiwar Wata na Zainab Sulaiman daga jihar Kano wanda kuma Badriyya Kalarawi ta karanta.
Marubuciyar ta rubuta labarin ne a matsayin hannunka mai sanda ga wasu matan, inda take so su fahimci cewa 'don Allah ya yi ki baƙa ba haka yana nufin ba ki da daraja ko kyau ba ne.'
Ana cewa duk wanda ya raina tsayuwar wata ya hau sama ya gyara, ita ma jarumar labarin ta raina tsayuwar nata watan ne, ta ce launin baƙar fatarta da Allah ya yi mata bai yi ba, don haka ta hau ta gyara ta hanyar rina kanta da fari irin na kanti da ta yi.
To amma me hakan ya haifar mata?
Nadama ce mai girma wadda sai da ta gwammace da za a mayar da ita launinta na farko.