Ƴan wasan Afirka shida da suka sauya kulob a bana

Hotunan Noussair Mazraoui da Victor Osimhen da Serhou Guirassy a haɗe.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Noussair Mazraoui da Victor Osimhen da Serhou Guirassy sun fara shirye-shiryen ganin sun ba maraɗa kunya a sababbin ƙungiyoyin da suka koma.
    • Marubuci, Richard Parr
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A yanzu da dawowa wasannin manyan gasannin Turai a wannan makon bayan hutun da aka tafi na wasannin tawagogin ƙasashe, yanzu ƴan wasan Afirka da suka canja kulob ne suke ƙokarin ganin sun fara da ƙafar dama.

Victor Oshimhen wanda ya zura ƙwallo a wasan da Najeriya ta lallasa Benin da ci uku da nema a wasan neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka gaba a cikinsu.

Ɗan wasan gaban ya koma Galatasary ne bayan kai-koma da aka sha a game da makomarsa har ta kai yawancin manyan gasannin Turai sun rufe kasuwancin ƴan wasa.

An ci kasuwar ƴan wasa da dama a kakar bana, ciki har da Gasar Saudi Pro League da ta sake kwasa, sannan tsohon ɗan wasan Najeriya Victor Moses wanda ya koma tala leda a ƙungiyar Luton Town da ke Ingila.

BBC Sport Africa ta yi nazarin fitattun ƴan wasan Afirka da suka canja kulob a makonnin da suka gabata.

Victor Osimhen (Napoli zuwa Galatasaray)

An samu tsaiko ne a kan makomar Osimhen saboda zaman tankiyar da aka samu tsakanin ɗan wasan da Napoli, har ta kai ya koma Turkiyya.

An yi hasashen ɗan wasan zai koma ƙungiyar PSG ta Faransa ne ko ɗaya daga cikin manyan tawagogin premier ta Ingila ko kuma Saudiyya.

A ƙarshe dai yanayin tsaikon da aka samu ya sa dole ɗan wasan mai shekara 25 ya yi sahun wani gwarzon ɗan wasan na Afirka Didier Drogba, wanda shi ma ya taka leda a Galatasary.

Oshimhen ya sanya hannu a kwantiragin aro na shekara ɗaya.

A cikin kwantiragin an amince cewa a tsakiyar kaka wato a Janairu idan wata ƙungiya ta yi zawarcinsa zai tafi, amma abubuwa ba su tafi kamar yadda yake so ba, dole zai oma Napoli.

Yanzu tambayar da ake yi ita ce shin Gwarzon ɗan wasan na Afirka wanda yake taka leda da takunkumin fuska zai iya dawowa ganiyarsa daga wannan aron?

Wilfried Zaha (Galatasaray zuwa Lyon)

Sai a sa'o'in ƙarshe ne aka samu nasarar sayar da ɗan wasan na Ivory Coast zuwa ƙungiyar Lyon ta Faransa a matsayin aro na kaka ɗaya.

Ɗan wasan mai shekara 31 ya lashe Gasar Turkiyya a kakar bara, amma kuma da zura ƙwallo 10 da ya yi a wasa 42 da ya buga - ciki har da zura ƙwallo a ragar Manchester United a Gasar Zakarun Turai - a ƙarshe-ƙarshen kakar ba a cika fara wasa da shi ba.

Yanzu tsohon ɗan wasan na Crystal Palace zai so ya samu lokaci sosai domin nuna bajintarsa a Faransa, inda ake tunanin zai zama abin koyi na matashin ɗan wasan gaban Najeriya Gift Orban.

Bayan rashin samun nasara a Istanbul, shin Zaha zai dawowa ya cigaba da rawar gaban hantsina a Faransa kamar yadda aka saba ganinsa a Crystal Palace?

Serhou Guirassy (Stuttgart zuwa Borussia Dortmund)

Ɗan wasan gaban Borussia Dortmund Serhou Guirassy yana atisaye.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙididdiga ta nuna cewa Guirassy yana da ƙwallo ɗaya ne a duk minti 79 na wasa a Stuttgart.

Har yanzu magoya bayan Borussia Dortmund ba su fara ganin ɗan wasan gabansu Guirassy a filin wasa ba saboda rauni da ya ji a wasannin sharar fage.

Amma ɗan wasan na ƙasar Guinea - wanda ya zura ƙwallo 28 a wasa 28 da ya buga a kakar bara zun taimaka wa ƙungiyar samun gurbin a Gasar Zakarun Turai - yanzu ya dawo atisaye sosai, kuma zai fara wasa a wannan watan.

Ɗan wasan wanda ya fi daɗewa a ƙananan gasanni wato na rukuni na biyu a ƙasashen Faransa da Jamus, ya kasance wanda ya fi zura ƙwallaye na biyu a gasannin a kakar 2023-2024 bayan Harry Kane.

Daraktan Wasanni na Dortmund Sebastian Kehl ya bayyana ɗauko ɗan wasan a farashin fam miliyan 15 ($11.4m) a matsayin kasuwanci mai kyau.

"Serhou cikakken ɗan wasan gaba ne, wanda yake da matuƙar haɗari wajen zura ƙwallo," inji shi.

Yanzu abin jira a gani shi ne, shin Guirassy zai iya maimaita bajintar da ya yi a bara a bana?

Noussair Mazraoui (Bayern Munich zuwa Manchester Utd)

Kocin Manchester United ya ɗauko ɗaya daga cikin zaratan ƴan wasan da ya yarda da su wato Mazraoui ne domin ƙarfafa tsaron tawagar.

Ɗan wasan mai shekara 26 yana cikin ƴan wasan Maroko da suka kai wasan kusa da ƙarshe a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022.

Yana cikin ƴan wasa biyu da ƙungiyar ta ɗauko a kan fan miliyan 60 ($45.6m) tare da ɗan wasan bayan Netherland, Matthijs de Ligt.

"Erik na cikin waɗanda suka raka muhimmiyar rawa wajen zamowata ƙwararren ɗan ƙwallo, shi ya sa nake farin cikin sake haɗuwa da shi a yanzu da na kai matuƙa."

Ba dukkan ƴan wasan Ajax da Ten Hag ya kawo Old Trafford ba ne suka samu nasara, amma shin Mazraoui zai iya taimakon kocin nasa wajen rage masa zafi a Manchester United?

Noussair Mazraoui zai jefa ƙwallo a wasan Manchester United da Fulham.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Da Mazraoui aka fara dukkan wasannin premier na Manchester United na kakar bana.

Kelechi Iheanacho (Leicester City zuwa Sevilla)

..

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar ta Spain ta maye gurbin wani ɗan wasan Afirka ɗin ne ɗan ƙasar Maroko Youssef En-Nesyri da ya koma Fenerbahce.

Sevilla ta ɗauko Iheanacho a kan kwantiragin shekara biyu.

Ɗan wasan mai shekara 27 ya zura ƙwallo 61 a wasa 232 da ya buga a zamansa na shekara bakwai a Leicester, inda ya lashe Gasar Kofin Ƙalubale wato FA a 2021, sannan yana cikin ƴan wasan da suka taimaka wa ƙungiyar wajen dawo da ita gasar premier a bana.

Sevilla ta ƙare a mataki na 14 ne a kakar bara, wanda shi ne mafi muni tun bayan dawowarta Gasar La Liga a 2001.

Yanzu Iheanacho zai so ya ƙara wa ƙungiyar armashi da zura ƙwallaye domin dawo da ƙungiyar matakin da take a nahiyar Turai.

Jordan Ayew (Crystal Palace zuwa Leicester)

Jordan Ayew yana murnar zura ƙwallo a wasan Leicester City Tranmere a kofin Carabao

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jordan Ayew ya zura ƙwallo a wasan Leicester City da Tranmere Rovers a wasan kofin Carabao

Bayan Iheanacho ya koma Sevilla, sai Leicester ta ɗauko ɗan wasan ƙasar Ghana Ayew daga Crystal Palace.

Ɗan wasan mai shekara 32 ya shiga yarjejeniya shekara biyu a kan Fan miliyan 5.

Ayew ya yi shekara shida a Palace, inda ya zura ƙwallo 23 a wasa 212 da ya buga.

"Duk da cewa na kai shekara 32 yanzu, amma kullum ƙara koyon abubuwa nake yi domin ƙara ƙwarewa," inji shi.

Duk da cewa tawagar Black Stars ta Ghana maki ɗaya kacal ta samu a wasa biyu na neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Afirka ta 2025, Ayew zai yi ƙoƙarin ganin ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen tabbatar da Leicester City ta cigaba da zama a gasar premier.