Martinez ya kai Argentina zagayen kusa da ƙarshe a gasar Copa America

Martinez

Asalin hoton, Getty Images

Emi Martinez ya ƙara nuna amfaninsa a tawagar Argentina bayan da ya kaɓe bugun finariti har biyu, lamarin da ya taimaka wa ƙasarsa kai wa zagayen kusa da karshe a gasar Copa America.

Wannan bajintar ta golan Aston Villa, ta bai wa Argentina nasara da ci huɗu da biyu a bugun fenariti tsakaninta da Ecuador bayan an tashi ɗaya da ɗaya.

Ba wannan ne karon farko da Emi Martinez ke raba ƙwai da dutse a bugun fenariti ba saboda a gasar cin kofin duniya a 2022, shi ne ya taimaki Argentina ta samu nasara a kan Faransa a wasan ƙarshe.

Sannan ya yi irin haka a wasan da Aston Villa ta doke Lille a gasar Europa Conference League.

"Na faɗa wa ƴan wasanmu ban shirya komawa gida ba," in ji Martinez.

"Mu ne zakarun duniya ya kamata a ci gaba da damawa da mu".

Shi ma kocin Argentina, Lionel Scaloni ya jinjina wa Martinez saboda gudunmuwar da ya bayar inda ya ce "Golanmu shi ne makullin".