Lafiya Zinariya: Ko kun san ciwon kan da ya fi damun mata?
Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce matsalolin ciwon kai sun shafi kimanin kashi 40 cikin dari na al'umma a faɗin duniya.
Ko kuma kimanin mutum biliyan 3.1 a shekarar 2021.
Wasu alkaluman da aka fitar kan kiwon lafiyar duniya a shekarar 2019, sun nuna cewa matsalolin ciwon kai su ne na uku, cikin cututtukan da ke janyo sauyin rayuwa zuwa rayuwa cikin nakasa, a faɗin duniya.
Cututtuka biyu da suka sha gaban matsalolin ciwon kai su ne, ciwon bugun jini da kuma cutar mantuwa. In ji WHO.
Sai dai a ƙasashe masu tasowa ciki har da Najeriya, masu fama da wannan matsalar da dama ba su san tana da magani ba.
Haka kuma masu fama da ciwon kai ƙalilan ne, aka iya gano ainihin abin da ke damunsu sakamakon samun kulawar ma'aitan lafiya.
Dr. Jamila Aliyu Dikko wata likitar ƙwaƙwalwa ce da ta ƙware a fannin ciwon kai, wadda ke aiki a Najeriya ta ce akwai nau'uka 300 na ciwon kai.
To ko waɗanne ne suka fi damun mata? Ku latsa makunnin da ke sama domin jin ƙarin bayani kan hakan.