Gane Mini Hanya : Kan shirin Jigawa na sayen amfanin gona 18-01-2025
Gane Mini Hanya : Kan shirin Jigawa na sayen amfanin gona 18-01-2025
Gwamnatin jihar Jigawa, da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce tana shirin ƙaddamar da wani tsari na sayen amfanin gona daga hannun ƙananan manoma don kawar da rashin tabbas ko sayar da kayan a farashi mai rahusa.
Haka kuma ta yi alƙawarin samar da taraktocin haya ga ƙananan manoma inda za su riƙa biyan 'yan kuɗi kaɗan a yi musu aiki a gonaki.
Gwamnan jihar ta Jigawa, Mallam Umar Namadi ya yi wa Zahraddeen Lawan bayani kan shirin a filin na Gane Mini Hanya na wannan makon.