Ra'ayi Riga: Yadda ƴanbindiga ke ƙwace wasu yankuna a Borno da Plateau
Ra'ayi Riga: Yadda ƴanbindiga ke ƙwace wasu yankuna a Borno da Plateau
Shirin Ra'ayi riga na wannan mako ya tattauna kan batun komawar hannun agogo baya a yaƙin da Najeriya ke yi da ta'addanci da ƴan bindiga a jihohin Borno da Filato, kamar yadda gwamnonin jihohin suka fito suka koka.
A baya-bayan nan ne dai gwamnonin jihohin Borno da Plateau a arewacin ƙasar suka fito fili suka yi ƙarin cewa wasu yankunan jihohinsu sun kuɓuce da hannunsu, tare da faɗawa hannun Boko Haram ko kuma ƴanbindiga.
Shin hukumomi sun yi zaune da siddi ne matsalar tsaron ta sake dawowa?
Mene ne hatsarin dawowar ƙungiyoyi irin na Boko Haram da ƙarfinsu a Najeriya
Ta yaya za a shawo kan wannan matsalar?
Waɗannan na cikin batutuwan da muka tattauna a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.