Me ya sa shari'ar zaɓen gwamna ta hana 'yan siyasar Kano barci?

'Yan APC a Kano

Asalin hoton, Facebook/Kamal Ibrahim Hotoro

Bayanan hoto, Cikin abubuwan da 'yan siyasar Kano ke yi har da yanka dabbobi don neman taimakon Allah a shari'ar gwamnan jihar
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Rashin tabbas da kuma fargabar abin da ka iya faruwa da rayuwarsu ba tare da gwamnati ba na ci gaba da hana 'yan siyasar jihar Kano barci.

Wannan ba sabon abu ba ne a kowace siyasa musamman ta jihohi a Najeriya, inda 'yan adawa ke ruguntsimin komawa jam'iyya mai mulki ba tare da wata kunya ba da zarar an kayar da tasu a akwatin zaɓe.

Sai dai abin da ya bambanta ta Kano da sauran shi ne, jam'iyyar NNPP mai mulki da APC mai adawa na cikin fargabar samu ko rasa mulkin yayin da Kotun Ƙolin Najeriya za ta fara zaman sauraron ƙarar da NNPP ɗin ta ɗaukaka.

Bugu da ƙari, APC ta shafe kusan shekara 10 tana mulkin Kano - tun daga lokacin Rabiu Kwankwaso har zuwa shekara takwas na Abdullahi Ganduje - kafin NNPP ta doke ta a 2023. Saboda haka, kowace jam'iyya na ganin kanta a matsayin mai mulki har zuwa ranar da kotu za ta yanke hukunci.

Ɓangarorin biyu za su san makomarsu ne nan gaba a kotun daga-ke-sai-Allah-ya-isa bayan hukuncin kotuna biyu na baya sun soke nasarar NNPP a zaɓen na watan Maris tare da bai wa Nasiru Gawuna nasara a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano.

An ga yadda 'yan siyasar suka fara rige-rige wajen gudanar da yanke-yanke da salloli don neman nasara a shari'ar ta kotun ƙoli, wadda ba ta saka ranar yanke hukuncin ba, amma ana sa ran za ta zauna a watan Disamba.

Kazalika, 'yan siysar NNPP da na APC na jefa wa juna zargin bai wa kotuna cin hanci don a murɗa hukuncin ya dace da kowannensu, duk da cewa suna musantawa.

Babu abin da aka fi tattaunawa a kai tsakanin mutane a wuraren zama kamar yanayin siyasar da jiharsu ke ciki, inda wasu ke tausaya wa NNPP wasu kuma ke goyon APC.

Zanga-zanga, sallah, da addu'o'i

'Yan kwankwasiyya da ke zanga-zanga

Asalin hoton, Facebook/Justice for Kano Movement

Bayanan hoto, Magoya bayan jam'iyyar NNPP mai mulkin Kano sun shafe kwanaki suna zanga-zangar neman a yi musu adalci a hukuncin kotu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun daga ranar 17 ga watan Nuwamba - lokacin da kotun ɗaukaka ƙara ta jaddada nasarar Nasiru Gawuna a hukuncinta - 'yan siyasa da ma mazauna Kano suka shiga cikin zaƙuwa da zullumi.

Hakan ya sa suka shiga gudanar da abubuwa da daban-daban na neman nasara.

Kusan kwana uku ke nan a jere magoya bayan NNPP - waɗanda aka fi sani da 'yan Kwankwasiyya - suna gudanar da zanga-zangar nuna ɓacin ransu ga shari'o'i biyun da suka gabata.

A ranar 20 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta Kano ta ce Gawuna ne ya lashe zaɓen, wata ɗaya bayan haka kuma kotun ɗaukaka ƙara ta jaddada hukuncin.

"Yancinmu ne [zanga-zanga], duk da cewa jagororinmu sun hana mu, mu kuma mujn ce ba za mu fasa ba wallahi," kamar yadda wata mai zanga-zanga mai suna Fatima ‘Yar Baiwa ta faɗa wa BBC ranar Litinin.

Dandazon ‘yan kwankwansiyya maza da mata ne - sanye da jajayen tufafi riƙe da kwalaye suka yi zanga-zangar a yankin Mariri na ƙaramar hukumar Kumbotso.

'Yan kwankwasiyya da ke taron addu'a

Asalin hoton, Nasara Radio

Bayanan hoto, Magoya bayan NNPP sun yi salloli da addu'o'i a mazaɓar Gwamnan Kano Abba Kabir

A gefe guda kuma, wasu magoya bayan sallah da addu'a suka runguma. Wasu ma har da yanka dabbobi da zimmar Allah ya ba su nasarar cigaba da zama a kan mulkin Kano.

Gomman magoya bayan Kwankwasiyya ne suka taru a mazaɓar Gwamna Abba Kabir da ke Diso Chiranci, inda suka yi salloli da saukar Ƙur'ani.

'Yan APC ba su gudanar da zanga-zanga ba kamar abokan hamayyarsu, amma ba su gaza ba wajen salloli da addu'o'i.

'Yan APC da ke addu'o'i

Asalin hoton, Facebook/Kamal Ibrahim Hotoro

Bayanan hoto, Magoya bayan Gawuna da APC ma sun yi saukar al-Ƙur'ani a mazaɓarsa ranar a ƙarshen mako

A ranar Lahadi ma, magoya bayan Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC sun gudanar da addu'o'u da saukar al-Ƙur'ani a zawiyar Zawiyar Sheikh Hassan Gawuna.

Haka nan, sun yanka dabba da zimmar Allah ya bai wa ɗan takararsu nasara a mazaɓar tsohon mataimakin gwamnan da ke Gawuna a ƙaramar hukumar Nasarawa.

Magoya bayan APC a Kano

Asalin hoton, Facebook/Kamal Ibrahim Hotoro

Za mu kai kwamishinan shari'a kotu idan bai janye zarginmu da ba da cin hanci ba - APC

Abdullahi Abbas

Asalin hoton, Facebook/Abba K Naisa

Bayanan hoto, Abdullahi Abbas ne shugaban APC a Kano

Shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya bayar da wa’adin sa’a 48 ga kwamishinan shari’a na jihar, Haruna Isa Dederi, ya janye zargin cin hancin da ya yi iƙirarin shugabannin APC na Kano sun bayar don tanƙwara shari'a ko kuma su kai shi kotu.

Wata wasika da Abdullahi Abbas ya rubuta ga Dederi, kuma aka fitar da ita ga manema labarai ranar Lahadi a Abuja, ta ce babban jami'in shari'a na jihar Kano ya zargi shugabannin APC da yin tankwara shari'ar gwamnan Kano a kotun ƙorafin zaɓe ta jihar, da kuma hukuncin alkalan kotun ƙoli da suka kori nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyya NNPP a zaɓen wajen Maris.

Abbas ya ƙara da cewa, kwamishinan shari'ar ya tozarta alƙalan kotun ɗaukaka kara da cewa "bisa ga bayanan da muka samu an yi katsalandan daga masu iko".

“Tun bayan kalaman da ka yi, na samu kiraye-kirayen waya da sakonnin waya masu yawa daga ‘yan uwa da abokai har ma da abokan aikina da abokan arziki suna neman karin bayani a kan ko gaskiya ne jam’iyyata ta yi katsalandan a hukuncin da kotun ta yanke na ɗaukaka kara," in ji wasiƙar.

"Na kuma samu barazana iri-iri ciki har da yunkurin kai hari gidana da ke Kano."

Da yake mayar da martani, Dederi ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa bai ga wata wasika daga shugaban jam’iyyar APC ba, yana mai cewa raɗe-raɗi ne kawai.

"Na ji wasu na cewa, sun gani a shafukan sada zumunta amma ba ni da abin cewa," a cewarsa.

'Zanga-zanga da sunan 'yan kasuwar Kano'

A gefe guda kuma, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta bankaɗo wani shiri da wasu mutane ke yi na tayar da hankali a jihar da sunan ƙungiyoyin 'yan kasuwa na jihar.

Wata sanarwa da Kwamishinan 'Yan Sanda Mohammed Usaini Gumel ya fitar ta ce tuni mutanen suka fara shirya taro da sunan yin addu'o'i a ƙananan hukumomin Bebeji da Kura da Ungoggo.

"Sai dai kuma tuni 'yan kasuwar Kantin Kwari, da Sabongari, da Kofar Wambai suka nesata kan su daga wannan zanga-zangar suna masu cewa ba su suka shirya ta ba," in ji kwamishinan.

A makon da ya gabata 'yan sanda sun yi arangama da wasu magoya bayan NNPP da ke zanga-zanga, inda suka harba musu hayaƙi mai sa hawaye.

Abin da ya ƙara ɗumama yanayin

Shekaru da dama an san siyasar Kano da ɗumi sosai ko da ba lokacin zaɓ ba ne.

Hakan ta sa jihar ta yi fice a fannin siyasa ta yadda duk jam'iyyar da ke mulkinta ke tasiri har a siyasar ƙasa baki ɗaya. Jihar Kano kaɗai jam'iyyar NNPP ta lashe a zaɓn gwamna na watan Maris, ganin yadda take fafatukira kare kujerar tata ɗaya tilo bai kamata ya bai wa mutane mamaki ba.

"APC tana ganin bai kamata a ƙwace mulki daga hannunta ba bayan shekara takwas tana mulki, sannan kuma ita vce babbar jam'iyya a yankin arewa maso yamma baki ɗaya," a cewar Malam Kabiru Sufi - mai sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya.

Yana ganin cewa ƙarin dalilin da ya sa yanayin zafafa a ɓangaren NNPP, tana ganin tana ɗan takararta na shugaban ƙasa daga Kano yake, kuma Kanon ce kaɗai gare su.

"Haka nan, APC na ganin cewa duk da an fi su yawan ƙuri'u duk wanda ya samu ƙuri'a sama da 800,000 to karansa ya kai tsaikon da bai kamata ya haƙura ba."

Malam Sufi na ganin duka ɓangarorin biyu sun sauka daga kan ainahin abin da ya kamata su yi.

"Wasu na ganin ba abin da ya kama suke yi ba. Da za su koma ƙoƙari wajen yin nasara a gaban kotu da zai fi musu saboda yanzu ba lokacin neman goyon bayan mabiya ba ne," in ji shi.