Abin da ya sa 'yan wasa ke gamuwa da bugun zuciya

.

Asalin hoton, Getty Images

Shahararren dan wasan kwallon kafar Amurka, Damar Hamlin, shi ne dan wasa na baya-bayan nan da ya gamu da matsalar bugun zuciya yayin buga wasa.

Dan wasan mai shekara 24 ya fadi kasa lokacin da ake buga wasa bayan da suka yi karo da wani dan wasa mintoci kadan a tashi wasa.

Likitoci sun tabbatar da cewa ya gamu da bugun zuciya – wanda hakan ke nufin zuciyarsa ta daina bugawa yadda ya kamata na samar wa wasu sassan jikin jini.

Likitocin sun yi kokari wajen ganin sun ceto rayuwarsa a cikin filin.

Yanzu dai yana kwance cikin mawuyacin hali a asibiti.

Likitoci da ke jinyarsa ba su bayyana takamaimen matsalar da take damunsa ba.

Wani abu da ke janyo bugawar zuciya shi ne kaduwa wanda ake kira da commotio cordis.

A wannan yanayi, idan wani abu ya bugi kirji, hakan zai iya janyo bugawar zuciya, inda zuciya ba za ta yi aiki yadda ya kamata ba.

Wannan wani na’u’in bugun zuciya ne na daban wanda ke faruwa idan jijiyoyi suka daina samar da jini wanda hakan kan janyo matsala ga zuciya saboda nauyin bugu.

Ba a dai san irin raunuka da Hamlin ya samu ba a cikin zuciyarsa daga karon da ya yi da wani dan wasa sannan ko zuciyarsa ta samu matsala.

Wata matsala ta zuciya da ‘yan wasa ke fuskanta shi ne cuta ta zuciya da ke shafar jijiyoyi.

.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mutane da ke da irin wannan matsala za a iya ganinsu cikin koshin lafiya ba tare da wasu alamu da ke nuna cewa suna fama da wata lalura ba.

Yanayi ne da ke sanya jijiyoyin zuciya ƙara girma, inda hakan ke sakawa da wuya jini ya kai zuwa zuciya, wanda hakan ke nuna akwai wata matsala a kasa.

Masu gwagwarmayar adawa da rigakafi a kafofin sada zumunta sun dora laifin matsalar bugun zuciyar Hamlin kan alluran cutar korona duk da cewa ba su bayar da wata hujja ba.

Sun kuma tattara alkaluman ‘yan wasan da suka mutu domin ƙarfafa hujjarsu.

Sai dai, a cewar wani bincike na 2016, akwai akalla mutane 100 zuwa 150 da ke mutuwa a Amurka sakamakon bugun zuciya a kowace shekara yayin buga wasanni.

Ba a dai gano sakamakon rigakafi na Hamlin ba.

A watan Maris din 2022, Hukumar shirya gasar kwallon kafa ta Amurka, ta ce an yi wa kashi 95 na ‘yan wasan rigakafin cutar korona.

Hamlin dai ba shi ne dan wasa na farko ba da ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da wasa.

Shi ma dan wasan ƙasar Denmark, Christain Eriksen, ya gamu da bugun zuciya a shekarar da ta gabata yayin buga wasa a gasar Euro 2020, inda ya kusa rasa ransa.

Likitoci sun yi amfani da wata na’ura domin farfado da zuciyarsa, inda ta dawo aiki yadda ya kamata.

Tun daga wancan lokaci aka samar da wata karamar na’ura mai suna ICD domin ci gaba da duba zuciyarsa.

.

 Eriksen ya ce babu ko da wani a cikin iyalansa da ya taba gamuwa da matsalar bugun zuciya, saboda ana masa gwaji iya rayuwarsa ta kwallo kamar sauran manyan ‘yan wasa.

A 2012, wani dan wasa mai suna Fabrice Muamba, ya yanke jiki ya fadi a cikin fili a lokacin da zuciyarsa ta daina aiki.

An samar da na’urori 15 domin farfado da zuciyarsa.

Idan aka bai wa mutum agajin lafiya ta gaggawa yakan samu sauki amma ba ko yaushe ake samun nasarar ceto rayuwar mutum ba.

A cewar binciken gidauniyar Cardiac Risk in the Young, mutum 12 ‘yan kasa da shekara 35 ke mutuwa a Birtaniya a kowane mako sakamakon bugun zuciya.