'Yadda gungun maza suka yi min fyaɗe a ranar aurena'

Asalin hoton, Terry Gobanga
A lokacin da aka wayi gari ba Terry Gobanga ƴar asalin Kenyaa ba, wadda a lokacin ake kiranta da suna Terry Apudo a wajen bikinta ba, babu wanda ya yi zaton sace ta aka yi ko fyaɗe aka jefar da ita a hanya.
Hakan kuwa aka yi, domin sace aka yin, aka mata fyaɗe, aka jefar, amma ta tsira ranta.
Ga labarin Terry nan, kamar yadda ta bayar da kanta.
Biki ne aka tsara shagulgula sosai, kuma a lokacin ni fasto ce, don haka an gayyaci dukkan ƴan cocinmu da ƴan'uwa da abokan arziki.
Ni da wanda zan aura Harry mun kasance cikin farin ciki domin ganin za mu cika burinmu na zama da maiji a cocin All Saints Cathedran da ke babban birnin Nairobi ta Kenya.
Ana gobe bikin ne na lura akwai wasu kayan sakawa na Harry a gidana, kuma a ciki akwai waɗanda yana buƙatarsu a ranar bikin. Don haka sai wata ƙawata ta ce za ta kai masa gida. Sai muka tashi da safiya na tuƙa mota zuwa wajen hawa mota.
Da zan koma gida, sai na ci karo da wani mutum a zaune a kan motarsa, wanda ya kama ni, ya tura ni cikin motarsa, a ciki akwai wasu mutum biyu, sai suka ja motar suka tafi da ni.
Sai suka ɗaure min baki, na yi ta ƙoƙarin ƙwacewa, har na samu da ƙyar na yi ihun cewa, "yau ranar aure na ce." wanda ina rufe baki na fara jin bugu, sai ɗaya daga cikin su ya faɗa min in ba su haɗin kai ko su kashe ni.
Sai suka fara min fyaɗe. A lokacin na san mutuwa zan yi, sai na ciji ɗaya daga ciki a gabansa, inda ya tsala ihu, sannan ya fara buguna, wani ya fara taya shi. Sai suka buɗe motar suka jefar da ni.
Sun jefar da ita ne kimanin tafiyar awa shida daga Nairobi.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani ƙaramin yaro ne ya ga lokacin da aka jefar da ni, sai ya kira kakar shi, sannan mutane suka taru.
Ko da ƴansanda suka iso wajen, babu wanda ya damu da duba ni, suna tunani ai na riga na mutu. Sai suka nannaɗe suna yunƙurin kai ni wajen adana gawarwaki.
Ana hanya ne na yi nishi, sai wani ɗan'sanda ya tambaye ni, "kina raye?" sai suka juya aka tafi da ni asibiti.
An kai ni asibiti cike da jini da fuska a kumbure, amma sai wata ma'aikaciyar asibiti ta ce ta lura kamar akwai alamar biki a tattare da ni.
Sai ta ce a tafi coci-coci da ke kusa a tambaya ko akwai amarya da ake nema.
Sai na ji tana waya tana tambayar ko akwai wata amarya da ake nema, inda aka amsa mata cewa akwai wata amarya da ake nema da ya kamata a ɗaura mata aure da misalin ƙarfe 10 na safe, amma a ganta ba.
A can da lokacin biki ya yi ba a ganni ba, sai hankalin iyayena ya tashi, inda mutane suka fara nemana ruwa a jallo.
Sai aka fara maganganun ko dai na fasa auren ne? wasu kuma na tambayar me yake faruwa haka?

Asalin hoton, TERRY GOBANGA
Bayan wasu awanni sai aka cire kwalliyar bikin, domin wasu su fara nasu biki, shi kuma Harry aka bar shi a cikin tsaka mai wuya.
Da Herry ya samu labarin inda, sai ya shi da iyayena suka zo asibitin, tare da dukka baƙin, sannan cikin ƙanƙanin lokaci ƴanjarida suka fara zuwa asibiti.
Sai aka mayar da wani asibitin domin samun kula mai kyau. A wannan asibitin likitoci suka ban labari muni a rayuwata, "sun miki rauni sosai har ya taɓa mahaifarki, don haka ba za ki iya haihuwa ba."
A haka Harry ya cigaba da cewa shi dai ya ji gani zai aure ni a haka, inda ya riƙa cewa, "ni zan yi jinyarta har ta samu sauƙi sosai."
Bayan kwana kaɗan, na fara buɗe idanuna, sai na gan shi a gefena yana ba ni haƙuri. Wasu sun riƙa cewa ai laifina ne da na fita a ranar bikina da safe, amma Herry da ƴan'uwana sun ban goyon baya sosai.
Ƴansanda ba su samu nasarar kama mutanen ba, an sha gayyata ta in duba waɗanda ake zargi, amma ban taɓa gani wanda ya yi kama da su har na gaji da zuwa.
Bayan wata uku da abin, sai sakamakon gwajina na cutar HIV ya fito, inda aka ce ban kamu ba, amma aka ce zan ƙara gwaji bayan wata uku. Amma duk da haka sai muka fara shirin sake wani bikin ni da Harry.
A watan Yulin 2005, wata bakwai bayan aukuwar ne muka sake wani auren da Harry, sannan muka tafi shaƙatawa.
Kimanin wata ɗaya bayan aurenmu, watarana bayan mun gama cin abincin dare, sai muka fara jin gajiya kaɗan-kaɗan.

Asalin hoton, JOSSE JOSSE
Kamar wasa sai zazzaɓi ya rufe mu, muna jin magana sama-sama, kwatsam sai na ji jikina ya mutu.
Na suma, shi ma Harry ashe ya soma. Sai na nemi taimakon maƙwabta bayan na yi amai, kawai sai na wayi gari a asibiti. Da na farka sai na samu kaina a asibiti a wani ɗakin.
Da na farka sai na tambaya ina mijina yake, aka ce min faɗa min yana wani ɗakin. Ni dai jikina bai ba ni ba, da na nace sai an faɗa min, sai aka faɗa min cewa ya rasu.
Nan take na sake shiga ruɗu. Da muka isa coci domin jana'izarsa, sai nake ta mamaki. Wata ɗaya kawai bayan aurenmu, yanzu ga shi a kwance ya rasu. Maimakon fararen kaya na biki, yau baƙaƙe na saka na jimami.
Sai mutane suka fara cewa ni annoba ce, har wasu suka fara hana yaransu zuwa kusa da ni, "har na fara yarda da abin da suke faɗa a game da ni."
Wasu kuma sai suka fara zargina da hannu a mutuwar mijina, wannan zargin ne ya ƙara ɗaga min hankali. Da wanne zan ji?
Bayan sakamakon gwajin gawa ya fito, sai aka ce guba muka ci a cikin abinci.
Watarana ina zaune a ƙofar gida ina kallon tsintsaye, sai nake ta zancen-zuci, "Allah me ya sa kake kula da tsuntsuya, amma ba ni ba?"
Sai na yanke shawara ba zan sake aure ba. Mijina ya rasu, kuma ba na tunanin zan iya sake jure wani zafin mutuwar mijin. Zafi mai raɗaɗin da ba zan so ko maƙiyina ya ji ba.

Asalin hoton, Terry Gobanga
Amma akwai wani mutum Tonny Gobanga wanda ya cigaba a zuwa wajena. Muna yawan tattaunawa kan rayuwa da tsohon mijina. Watarana sai ba mu yi waya ba kwana biyu a jere, sai na ji raina ya ɓaci, nan ne na gane na fara soyayya.
Tonny ya ce yana sona, sai na faɗa masa ya nemi mujalla ya karanta labarina, sannan ya sake tunani. Sai ya sake zuwa ya ce lallai yana sona.
Sai na faɗa masa cewa bayan wannan tiyar fa, akwai wata cacar, "ba zan haihu ba."
Sai ya ban amsa cewa, "haihuwa daga Allah. Idan mun samu shi ke nan, idan ba mu samu ba, ba komai."
Daga nan ne na amince zan aure shi.
Tonny ya je ya faɗa wa iyayensa, waɗanda suka fara murna, amma da suka samu labarina, sai suka cewa, "ba zai yiwu ka aure ta, annoba ce."
Mahaifin baban ya ƙi zuwa ranar bikin, amma duk da haka muka yi bikin. Baƙi 800 ne suka halarci bikin.
Shekara uku bayan auremu, sai na fara fargaba. Har na fara addu'ar, "Allah, ka kiyaye shi kada wannan ma ya mutu."
Da taron masu ibada suka mana, sai na fashe da kuka.
Amma shekara ɗaya bayan bikinmu, sai na fara zazzaɓi. Da na je asibiti a duba ni, abin ban mamaki, likita ya kalle, ya ce, "kina ɗauke da juna biyu."

Asalin hoton, Terry Gobanga
Ina ta tunanin duk da samu cikin, wataƙila ba zan iya haihuwa ba sai an min tiyata, amma kuma sai komai ya tafi ƙalau, inda na haifi yarinya mace da muka raɗa wa suna Tehille, bayan shekara huɗu na sake haifar Towdah.
Amma ni da sirikana mun shirya muna zumunci sosai.
Na rubuta littafi kan rayuwata mai suna 'Crawling Out of Darkness' domin ƙarfafa gwiwar mutane, sannan na buɗe gidauniya mai suna 'Kara Olmurani.'
Muna amfani da gidauniya wajen wayar da kai da ƙarfafa gwiwar waɗanda aka yi wa fyaɗe, sannan muka samar da gida za su riƙa zama domin samun kwanciyar hankali.











