Daruruwan mutane sun ce sun ga gilmawar tauraruwa mai wutsiya a Scotland da Ireland

Bayanan bidiyo, Daruruwan mutane sun ce sun ga gilmawar tauraruwa mai wutsiya a Scotland da Ireland
Daruruwan mutane sun ce sun ga gilmawar tauraruwa mai wutsiya a Scotland da Ireland

Daruruwan mutane ne suka bayar da rahotannin cewa sun ga gilmawar “tauraruwa mai wutsiya” a sararin samaniya a yankunan Scotland da Ireland.

Hukumar kula da sararin samaniya ta Birtaniya ta ce ta fara karɓar rahotanni a kan ganin gilmawar tartsatin wutar da misalin karfe 10 na dare agogon Birtaniya a ranar Laraba.

Masana Kimiyya suna a,mfani da bidiyon da mutane suka ɗauki faruwar lamarin don gano ko ɓurɓushin duwatsun da ke yawo a sararin samaniya ne, da kuma daga inda suka fito.