Mummunar illar da gubar dalma ke haifar wa 'yan Najeriya

Bayanan sautiDanna hoton sama ku saurari shirin:
Mummunar illar da gubar dalma ke haifar wa 'yan Najeriya

Masana lafiya a Najeriya na ci gaba da gargadi ga barazanar da gubar dalama ke yi ga rayuwar mutane sakamakon ayyukan masu ta’ammali da baturan motoci da na babura da aka gama amfani da su.

Dr Nasiru Sani Gwarzo - wanda ya yi rubutu kundinsa na shaidar kammala digiri na uku - na daya daga cikin wadanda suke yin wannan kiraye-kiraye.

A tattaunawarsa da Buhari Muhammad Fagge, Dr Gewarzo ya ce jihohi irinsu Kano da Jos da Zamfara na daga cikin wadanda ke fuskantar hatsarin gubar dalma a yanzu.