' Kuskure aka samu wajan cire sunan ɗan takarar mu'

Asalin hoton, Aminu Abdussalam Gwarzo Facebook
Jam'iyyar adawa ta NDC ta ce ta yi amanar cewa matsala ce aka samu wajan tantance jerin sunayen 'yan takara da Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar inda aka cire sunan Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin , ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar a Jihar Kano.
Ba a dai ga sunan Gwarzo ba a cikin jerin sunayen da hukumar ta fitar a karshen makon nan, wanda ya kunshi ƴan takara 17 daga jam'iyyun siyasa daban-daban.
Jam'iyyun All Progressives Congress (APC), da Peoples Democratic Party (PDP) da kuma African Democratic Congress (ADC) na daga cikin jam'iyyun da ke da 'yan takara a cikin jerin sunayen.
Dakta Dr Yusuf Ibrahim Kofar mata sakataren kungiyar kwankwasiya, ya shaidawa BBC cewa alamarin bai tayar mu su da hankali ba
''Na farko dai dan takararmu na gwamna a jihar Kano, kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya riga ya yi rajista da jam'iyyar NDC kuma ya yi ta akan lokaci, sannan abu na biyu kuma shi be yi rajista da jam'iyya biyu ba , a dan haka wannan hukunci na kotun koli ba zai taba shi ba'' in ji shi.
Ya ce bayan zaben fidda gwani shi ne ya samu nasara a zaben kuma sunansa aka kai hedikwatar jam'yyar ta kasa, daga nan aka kai sunansa ofishin hukumar zabe ta INEC.
''Duk an yi wannan kuma ba bu inda aka sami kuskure, duk sunansa ne, shi yasa mu ke ganin wannan wani kuskure ne aka samu wajen buga sunnayen ta komfuta wanda mu ke tunanin nan da ranar Litinin mai zuwa za a warware a gyra, in ji shi''
Dakta Yusuf Ibrahim Kofar ya ce uwar jam'yyar ta kasa ta tabbatar cewa ba ta yi kuskure ba kuma ta bi hanyoyin da suka da ce wajan gabatar da takardun ɗan takarar gwamna na jam'iyyar.
Ya kuma kara da cewa kawo yanzu hukumar zabe ta INEC ba ta turo mu su da takadar da ke dauke da jerin sunnayen 'yan takakarsu ba.































