Sulhu da 'yan bindiga ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro - Yariman Bakura

Bayanan sautiLatsa hoton da ke samma domin sauraron shirin
Sulhu da 'yan bindiga ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro - Yariman Bakura

Filin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna da Sanata Sani Yarima, tsohon gwamnan Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, mai fama da matsalar tsaro.

Tsohon mai neman takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC mai mulki, Yarima ya ce Shugaban Najeriya Bola Tinubu, wanda ya hau mulki a a watan Yuni, ya ɗauki matakan da sauran shugabanni suka gaza ɗauka.

Kazalika yana ganin yin sulhu da 'yan bindgar da ke kashe mutane a kullum a jiharsa ta Zamfara ita ce hanyar shawo kan lamarin.

Yariman Bakura