Gane Mani Hanya kan Dakatar da shugabannin wasu bankuna da CBN ya yi
Gane Mani Hanya kan Dakatar da shugabannin wasu bankuna da CBN ya yi
A Najeriya a daidai lokacin da tattalin arziƙin ƙasar ke cikin mawuyacin hali, wani mataki da babban bankin ƙasar – CBN ya ɗauka na rushe shugabannin waɗansu bankunan kasuwanci a ƙasar na ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki a wannan fannin.
A filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon, editanmu Aliyu AbdulLahi Tanko ya tattauna da ɗaya daga cikin masu hannun jari a bankin kasuwanci na Polaris, Alhaji Auwal Lawan, domin jin yadda suke kallon matakin da babban bankin Najeriya – CBN ya ɗauka a kan manyan bankunan uku cikin makon jiya.