Gane Mini Hanya: Tare da Bello El-Rufai 08/02/2025
Gane Mini Hanya: Tare da Bello El-Rufai 08/02/2025
Dan majalisar wakilan Najeriya daga mazaɓar Kaduna ta arewa, Hon Bello El-Ruafi ya ce babu daɗi irin takun-saƙar da ake samu tsakanin mahaifinsa, watau tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed Elrufai da kuma gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.
Honarabul Bello Nasir ElRufai ya ce 'yan siyasa ne ke ƙara rura rikicin domin biyan buƙatar kansu.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Bello El-Rufai ya soma da yin bayani kan yadda ya shiga takarar siyasa a jihar Kaduna.