Amsoshin Takardunku: Kun san dalilin kafa hukumar nukiliya ta duniya da ma ayyukanta?
Hukumar nukiliya ta duniya wata cibiya da aka kafa domin kulla da shirye-shirye da ayyukan sarrafa ma'adinin uranium da sauransu.
Sai dai shin me ya sa aka ƙirƙiri hukumar? kuma mene ne ayyukanta? tambayar da Adam Yusuf daga jihar Kebbin Najeriya ya aiko mane ke nan, inda ya buƙaci ƙarin bayani a kan ayyukan hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato IAEA domin sanin ayyukanta da hurumi da take da shi da ma tasirinta a kan ƙasashen duniya?
Wannan ya sa BBC ta tuntuɓi Dokta Sani Ma'azu, Babban Darakta a fannin fasaha a gidauniyar Fosriya, mai rajin habaka fasahar nukiliya a Najeirya, tare da haɗin gwiwar ma'akatar Man Fetir ta kasar.
To sai kuma tambaya ta gaba daga Al-Ameen Kabir daga Katsinan Najeriya, inda yake neman tarihin tsohon mai tsaron ragar tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, marigayi Peter Rufa'i.
Sai kuma tambayar da ta fito ne daga Adamu Yusuf Balantiya da ke fagge a jihar Kano, da ke neman ƙarin bayani a kan Miƙa, da dalilin da ya sa manya har ma da jarirai suke yinta? Na kuma mi'ka wannan tambayar ga Dokta Yusuf Khalifa, Babban Likita a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kanon Najeriya.
Waɗannan su ne tambayoyin da muka amsa a shirin wanda Ahmad Kabo Idris ne ya jagoranta.