Ra'ayi Riga: Kan ƙaruwar yi wa mutane kisan gilla a Najeriya
Ra'ayi Riga: Kan ƙaruwar yi wa mutane kisan gilla a Najeriya
Jama'a a wasu sassan arewacin Najeriya sun shiga tashin hankali da ɗimauta a 'yan makonnin nan, sakamakon samun ƙaruwar yiwa mutane kisan gilla a gida, waɗanda a mafi yawan lokuta makusantan mamatan ne ake zargi da aikata hakan.
Kashe-kashen da hukumomin tsaro ke ba da rahotannin an aikata cikin wasu jihohin arewa kamar Kano da Bauchi da kuma Jigawa, na ƙara jefa ayar tambaya a zukatan al'umma cewa: 'shin me yake faruwa ne?'
Shin mene ne ke janyo ire-iren wadannan kashen?
Kuma yaya girman matsalar take?
Wadanne matakai ne ya kamata a ɗauka domin magance irin wannan matsalar?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirin na wannan mako ya tattauna a kai.