Abin da ya sa ake yawan taƙaddama kan wajen da za a binne shugabannin Afirka

Asalin hoton, EPA
Cikin jerin wasiƙun da muke samu daga 'yan jaridar Afirka, 'yar Ghana Elizabeth Ohene ta yi rubutu game da irin rikicin da ake yi kafin binne shugabannin Afirka.
_______________________________________________________
Ba ni da tabbas ko zan iya ba da wani taƙadirin zance, amma ni ban taɓa sanin cewa kasancewar mutum shugaban wata ƙasa a Afirka zai iya haddasa rigima a ƙabarinsa ba idan ya rasu.
Na yi ta bin rikicin da ake yi game da inda za a binne tsohon Shugaban Ƙasar Angola José Eduardo dos Santos, wanda ya rasu a Sifaniya ranar 8 ga watan Yuli.
Shugaban ƙasar mai-ci João Lourenço da kuma matar Dos Santos na son a mayar da gawarsa gida don yi mata jana'izar ban-girma a ƙasaitacciyar maƙabarta ta musamman - abin da muke gani na girmamawa ga shugabanni a Ghana.
Amma 'yarsa mai suna Welwitschia "Tchizé" na son a yi masa jana'iza a killace kuma a binne shi a wani ƙabari na musamman a Sifaniya ta yadda 'ya'yansa za su iya ziyartarsa.
Ta ce wasu daga cikin 'yan uwanta na goyon bayan ƙudirin nata, waɗanda ke fuskantar zargin cin hanci kuma za a iya kama su da zarar sun saka ƙafa a Angola.
Ɗaya daga cikin 'ya'yan Dos Santos ya ce ba ƙasar ce ke da alhakin ɗaukar nauyin jana'izarsa ba kuma iyalinsa ne ya kamata su yanke hukunci.
Maganar cewa ko ƙasa na da iko kan gawar shugabanta ba sabon abu ba ne.
An samu irin wannan lamari a Zimbabwe a 2019 lokacin da Robert Mugabe ya rasu shekara kusan biyu da suka wuce bayan ya shekara 37 a kan mulki - inda shugaba mai-ci Emmerson Mnangagwa ya kawo ƙarshen mulkin nasa tare da goyon bayan sojoji.

Asalin hoton, Getty Images
Kowa ya yi tunanin za a bine shi ne a Filin Gwaraza na Ƙasa ( Heroes' Acre) da ke birnin Harare.
Ko ma dai mene ne, shi ne ya gina Heroes' Acre kuma ya binne da yawa daga cikin abokan gwagwarmayarsa, ciki har da Sally matarsa ta farko.
Mista Mnangagwa ya fara gina ƙabari na musamman don binne jagoran neman 'yancin, amma kuma iyalansa ba su amince da hakan ba ganin yadda aka kore shi daga mulki kuma abokan gwagwarmyarsa suka yaudare shi.
Bayan shafe makonni ana taƙaddama, iyalinsa sun yi nasara kuma an binne Mista Mugabe, jagora kuma gwarzo a Zimbabwe, a ƙauyensu ba tare da wani wakilin gwamnati ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hatta Kenneth Kaunda - shugaban ƙasa na farko bayan 'yancin kai a ƙasar Zambia kuma ɗaya daga cikin 'yan gwagwarmayar neman 'yanci - bai iya samun wurin da za a binne shi ba ba tare da rikici ba.
A cewar iyalinsa, ya so a binne shi kusa da matarsa ba inda gwamnati ta tanada ba.
Zuwa yanzu dai iyalin nasa ba su yi wata jayayya ba yayin da "KK" - kamar yadda ake kiran sa da shi - na ci gaba da kwanciya Embassy Memorial Park da ke Lusaka baban birnin ƙasar.
Daga gudun hijira zuwa girmamawa
Waɗannan rikice-rikice kan gawarwaki ba sabbin abubuwa ba ne. A nan Ghana, mun saba da irin wannan.
Shugaban ƙasarmu na farko Kwame Nkrumah ya rasu a Bucharest na Romania lokacin da yake jinya.
Da farko an binne shi a Conakry, Guinea bayan ya shafe lokaci yana gudun hijira a can. Daga baya aka mayar da gawarsa Ghana. An yi masa jana'izar gwamnati a Accra sannan aka binne shi a ƙauyensu na Nkroful.

Asalin hoton, EPA
A lokuta daban-daban za ka dinga jin iyalansa na cewa a dawo musu da gawarsa.
A 2012, shugaban ƙasarmu John Atta-Mills ya rasu yana kan mulki amma samun wurin da za a binne shi ya zama aiki.
Wasu daga cikin iyalansa sun nemi a kai gawarsa ƙauyensu, sai dai ba su samu wani goyon baya ba a lokacin.
An ƙyale wurin da gwamnati ta haƙa a matsayin ƙabarinsa saboda bai dace da shi ba. Daga baya aka mayar da shi wani wuri daban.
An tsara cewa wurin shaƙatawar da aka binne shi ya zama maƙabartar shugabannin ƙasa.
Tun daga wannan lokaci, wani shugaban ƙasar - Jerry Rwlings - yara su.

Asalin hoton, Getty Images
Ba kai shi wurin da aka binne Shugaba Atta-Mills kawai ba, iyalansa sun zargi gwamnati da aiwatar da hakan ba tare da izininsa ba.
An binne shi a maƙabartar sojoji da ke Accra tare da yi masa jana'izar girmamawa.
'Yan makonnid a suka wuce muka yi bikin cika shekara 10 da mutuwar Atta-Mills.
Har yanzu ana cecekuce a kan kushewarsa: wane ne zai kula da ita kuma me za a rubuta a kan ta.
Akwai kuma wasu daga iyalansa da ke son a tono gawarsa daga inda gwamnati ta binne shi a Accra zuwa ƙuyensu don a sake binne shi.
Saboda haka ina ganin ɗaya daga cikin matsalolin zama shugaban ƙasa a Afirka ita ce ba lallai a samu wurin da za a binne mutum ba idan ya rasu.











