Ra'ayi Riga: Kan ƙarin kuɗin ruwa da CBN ke yi a Najeriya 29/11/24

Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Ra'ayi Riga: Kan ƙarin kuɗin ruwa da CBN ke yi a Najeriya 29/11/24

A wannan makon ne babban bankin Najeriya CBN ya ƙara kuɗin ruwa na bashin da ake karɓa daga bankunan ƙasar zuwa kashi 27.50 cikin 100.

Wannan ne karo a shida da CBN ɗin ke ƙara kuɗin ruwa a wannan shekarar da muke ciki.

Ƙarin na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan ƙasar ke ci gaba da kokawa kan halin matsin tattalin arziki da suke ciki.

Tuni dai masu masana'atu da ɗaiɗakun mutane suka fara nuna rashin jin daɗinsu game da matakin.

Sai dai Babban Bankin Najeriyar ya ce ya yi ƙarin kuɗin ruwar ne domin rage kuɗin da ke yawo a hannun jama'a da shawo kan hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.

To ko yaya wannan ƙarin kuɗin ruwa da CBN ɗin ke yi, a kai a kai zai yi tasiri, ta yaya wannan mataki zai shafi harkokin kasuwancinku, da na rayuwar yau da kullum da na tattalin arzikin Najeriyar?

Waɗannan na daga cikin batutuwan da shirin na wannan mako ta tattauna a kansu.