Mene ne kusufi kuma nawa ake da shi a duniya?

Asalin hoton, NASA
Kusufi kan zama abubuwan kallo da nishaɗi na ilimin taurari ne.
Akwai dalilai masu karfi cewa duka rassan ɓangaren harkokin yawon buɗe ido sun tashi tsaye wajen kula da waɗanda ke son yin tozali da su.
Kusufi mai zuwa zai faru ne a ranar Litinin 8 ga watan Afrilu - kuma cikakken kusufin wata ne wanda kowa ke son gani.
Za a iya ganin kusufin ne daga duka arewaci da kudancin Amurka, Mexico da kuma Canada.
Yana faruwa ne a lokacin da Wata ya shiga ta cikin tsakiyar duniyar Earth ya kuma toshe duka hanyoyin hasken ranar da ke shiga kai-tsaye daga sararin saman Wata.
Hasken rana kan kai ga saman watan a kaikaice ta hanyar sararin duniyar ta Earth, ya kuma lulluɓe Watan da haske mai launin ja da rawaya da ruwan goro.
Kusufin shekara ta 2024 zai fara ne daga Penrhyn Atoll, da ke Tekun Pacific, wanda wani ɓangare ne na tsibirin Cook inda rana mai launin duhu za ta ci gaba da kasancewa har zuwa karfe 4:40 agogon GMT.
Daga nan inuwar Wata zai iya fitowa zuwa faɗin duniyar Earth sama da kilomita 2,500, inda zai bi ta Mexico da misalin karfe 6:07 agogon GMT zuwa kuma iyakar Rio Grande tsakanin Mexico da Amurka da karfe 6:27 agogon GMT.
Cikakken kusufin rana na faruwa ne a lokacin da Rana, da duniyar Earth da Wata suka hadu a wani yanayin da Watan ke lullube hasken rana baki daya.
A cikin dakikoki kaɗan (ko a wasu lokuta ma mintoci), sararin samaniya na kasancewa cikin tsananin duhu tamkar dare.
"Muna da kusufi iri biyu: akwai na Wata da kuma na Rana," kamar yadda Juan Carlos Beamín, wani masani kan ilimin taurari a Jami'ar ƙasar Chile, ya rubuta a cikin wani littafinsa kan sararin samaniya.
Amma kuma ya yi nuni da cewa: A fasahance akwai kusufi na uku wanda ya kunshi taurari biyu.''
Ga bayanan waɗannan kusufi iri uku da kuma nau'ikansu daban-baban:
Kusufin rana
A wasu lokuta, idan Wata ya zagaya duniyar Earth, yana tafiya tsakanin Rana da duniyarmu, tare da kare haske daga tauraro da kuma haddasa kusufin rana.
Ta wani gefen kuma, Watan kan yi inuwa a kan saman duniyar Earth.
Amma akwai kuma kusufin wata kashi uku, kana waɗannan sun bambanta da juna ne ta hanyar yanayi da kuma yawan yadda Watan ke lulluɓe Ranar.
Cikakken kusufin Rana
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikakken kusufin rana na faruwa ne a lokacin da Rana, da duniyar Earth da Wata suka haɗu a wani yanayin da Watan ke lulluɓe hasken rana baki ɗaya.
A cikin dakikoki kaɗan (ko a wasu lokuta ma mintoci), sararin samaniya ta kasance cikin tsananin duhu kamar ka ce dare ne.
A wasu bayanai na hukumar NASA, "cikakken kusufin rana kan faru ne a duniyar Earth saboda arashi na ilimin lissafi da kan faru ba zato ba tsammani'': Rana ta linka Wata sau 400 a faɗi, kana tana da nisan da ya linka na Wata sau 400.
"Wannan ilimin lissafi na nufin cewa a lokacin da suka haɗu sosai, Wata yana lulluɓe ɗaukacin saman Rana, tare da haddasa cikakken kusufi,'' in ji NASA.
Layin da ke bin diddigin inuwar Wata a zagayen sararin duniyar Earth ana kiran sa da ''path of totality" kana a cikin wannan karamin wuri ne ake iya ganin wannan ɗaukacin cikakken duhun.
A duka ɓangarorin biyu na zirin, ana iya ganin kusufin kaɗan daga tsawon dubban kilomita.
Kana kara nesa daga ɗaukacin zirin, sa'annan kara ganin karamin ɓangaren Ranar da Watan ke lulluɓewa.
"A bisa bincike mai zurfi, kusufin rana mafi daɗewa ka iya kai wa tsawon minti bakwai da dakikoki 32,'' in ji masanin ilimin taurari ɗan kasar Chile.
Dangane da faruwarsa kuwa, ba kasafai ake ganin sa ba kamar yadda za ku yi tunani: Ana samun kusufi sau ɗaya cikin watanni 18.
Abin da ba kasafai aka fi gani ba shi ne cikakken kusufin rana ya faru a wuri ɗaya kamar ya gabata, wani abu kuma da ke faruwa sau ɗaya cikin shekara 375.
Kusufin zobe

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da Wata ya kara yin nesa daga duniyar Earth sa'annan ya kara zama ''karami'', ba zai lulluɓe ɗaukacin Rana ba.
Don haka ana iya ganin Rana a yanayin fasalin zoɓe a zagayen Wata, kuma ana kiran wannan da suna annular solar eclipse ko kuma kusufin zobe.
Kamar dai a lokacin cikakken kusufin rana, lokacin wannan yanayi akwai wata 'yar hanya a inda ake iya ganin kusufin a yanayi mai kamar zobe.
Kamar yadda hukumar NASA ta bayyana, wannan kusufi galibi ya fi kowannen daɗewa, saboda za a iya kallon zoben har na tsawon minti goma.
Sai dai ba sa daɗewa na sama da watanni biyar ko shida.
A ranar 2 ga watan Oktoba ne ake sa ran ganin kusufin zobe na gaba a Arewaci da Kudancin Amurka, har ma da yankin Antarctica, Tekun Pacific, Tekun Atlantic da kuma wasu yankunan Afirka ta Yamma.
Tagwayen kusufi

Asalin hoton, Getty Images
Beamín ya bayyana cewa tagwayen kusufi ko hybrid eclipse wani yanayi ne da ke faruwa ''lokacin da Wata ke nesa da inda zai iya lulluɓe Rana gabaki-ɗaya, amma a yayin da yake kara tafiya, yana daɗa gusawa a hankali nesa da duniyar Earth kana ya dakatar da lulluɓe Ranar, ya rikiɗe ya koma kusufin zobe.''
"Zai kuma iya farawa daga kusufin zobe sannan ya matsa kusa ya zama cikakken kusufi," Beamín ya kara bayyanawa.
Kusufin na hybrid bai cika faruwa ba, wanda (kashi 4 bisa ɗari ne kawai a cikin duka kusufin rana da ke faruwa), kamar yadda cibiyar bincike ta Instituto de Astrofísica de Canarias (IAC) ta bayyana.
Lokaci na karshe da wannan kusufi ya faru shi ne ranar 20 ga watan Afrilun 2023, wanda aka gani a ƙasashen Indonesia, da Australia da kuma Papua New Guinea.
NASA ta bayyana cewa kusufi na gaba zai faru ne a watan Nuwamban 2031.
Kusufin Wata

Asalin hoton, AFP
Kusufin Wata na faruwa ne a lokacin da duniyar Earth ta shiga tsakanin Rana da Wata, tare da toshe haske.
Ta wani gefen kuma, lokacin kusufin wata, abin da muke gani a cikin inuwar duniyar Earth da ke kan saman farin Wata ne.
Kamar yadda cibiyar bincike ta Instituto de Astrofísica de Canarias (IAC) ta bayyana: ''Ganin kusufin Rana ya danganta da yanayin wurin da mutumin da ke kallo yake.
Akasarin haka na faruwa da kusufin wata: ana iya ganin faruwar hakan daga ko wane wuri a doron duniyarmu inda Wata ke tsakanin layin da ya raba sararin samaniya da duniyar Earth a lokacin kusufin.''
Jagoran ya kuma ce '' ba kamar sauran kusufai na Rana ba, inda tsarin matakan kusufin ya danganta ga daidai inda mutum ya ke, a kusufin wata wannan kan kasance iri ɗaya, koda kuwa daga ko a ina kake kallo.''
Kusufin wata ya kasu kashi biyu.
Cikakken kusufin wata
Lokacin cikakken kusufin wata, hukumar lura da binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ta bayyana cewa, Wata da Rana na fuskantar juna daga ɓangare biyu na duniyar Earth.
"Duk da cewa Wata na cikin inuwar duniyar Earth - NASA ta kara bayyanawa - wasu hasken ranar kan kai ga cikin Watan.''
Wannan hasken rana na bi ta cikin sararin duniyar Earth, wanda akasarin shuɗin haske - shi ya sa lokacin kusufin, Wata kan koma launin ja, wanda a wasu lokuta a kan yi masa lakabi da "blood moon" ko wata mai jini.

Asalin hoton, NASA
A cewar IAC, "saboda dogon layin da ke ratsa tsakiyar duniyarmu linki huɗu ne fiye da na wata, inuwarta kuma ta fi faɗi, don saboda cikakken kusufinsa zai kai tsawon mintoci 104."
Cikakken kusufin wata na gaba zai faru a watan Maris ɗin 2025, kuma za a iya ganinb sa a Tekun Pacific, Amurka, Yammacin Turai da kuma Yammacin Afrika.
Karamin kusufin wata lunar
Kamar yadda sunansa ya nuna, karamin kusufin wata na faruwa ne lokacin da ɓangaren Wata kaɗai ya shiga inuwar duniyar Earth.
Ya danganta da girman kusufin, baki ko ja - sai dai wasu lokutan yana iya zama mai launin gawayi - inuwa na iya fitowa a ɓangaren da ya fito ta yi duhu akan kusufin. Saboda bambanci tsakanin ɓangare mai dishi-dishi da kuma mai haske kan kusufin, wanda inuwar ba ta shafar sa.

Asalin hoton, Getty Images
A cewar NASA, yayin da ba kasafai ake ganin cikakken kusufin wata ba, karamin kusufin na faruwa akalla sau biyu a duk shekara.
Ana sa ran faruwar karamin kusufin wata na gaba ranar 18 ga watan Satumban 2024, kuma za a iya ganin sa a yankunan Amurka, Turai da kuma Afrika.











