Gane Mini Hanya: Manufofin gwamnatin Tinubu shekara biyu kan mulki
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dage a kan cewa manufofinta na tattalin arziƙi, sun ɗora Nijeriya a kan wani gwadaben gaskiya na samun bunƙasa, wanda komai daɗewa za a ga amfaninsa.
Jami'an Nijeriyar na cewa duk da yake har yanzu akwai matsin rayuwa da rashin tsaro a wasu sassa, amma dai ba shakka an samu ci gaba, kuma gwamnati za ta yi tsayin daka wajen ɗora a kan waɗannan nasarori.
Ƴan Nijeriya dai na ci gaba da kokawa a kan halin ƙunci da tsananin tsadar rayuwa, har ma wasu na ganin babu mafita face gwamnati ta dawo da tallafin man fetur, kuma ta farfaɗo da darajar naira.
Shi dai wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Ibrahim Masari ya ce gwamnatinsu za ta ci gaba da ɓullo da matakan da take ganin za su inganta rayuwar talaka, ba tare da sauraron masu suka ba.
A zantawarsu da abokin aikinmu Yusuf Tijjani, cikin filinmu na Gane Mini Hanya a wannan mako, Ibrahim Masari ya fara da zayyana muhimman ayyukan gwamnatinsu a cikin shekara biyu.