An yi jana'izar mutum 104 da suka mutu a fashewar tanka cikin juyayi
An yi jana'izar mutum 104 da suka mutu a fashewar tanka cikin juyayi
An yi jana'izar sama da mutum 100 da suka rasu sakamakon fashewar tankar mai a jihar Jigawa cikin juyayi.
Gwamna Umar Namadi da manyan jami'an gwamnati ne suka jagoranci jana'izar a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura, inda hatsarin ya faru.
An binne mutanen 104 a cikin babban ƙabari ɗaya da aka haƙa.