Lafiya Zinariya: Abubuwan da ke jawo wa mata ciwon kai

Bayanan sauti
Lafiya Zinariya: Abubuwan da ke jawo wa mata ciwon kai

Wasu alƙaluma na hukumar lafiya ta duniya, sun nuna cewa mata sun fi maza samun matsalar ciwon kai, a shekarar 2021.

Yayin da wasu likitoci suka ce matan sun fi samun nau'in ciwon da ake ji ta gefe guda na kai, wato Migraine.

Dakta Jamila Aliyu Dikko, wata likitar ƙwaƙwalwar da ta ƙware a fannin ciwon kai ta ce, mata na da wasu ƙwayoyin halitta da ke ƙaruwa ko su ragu, idan sun shiga wani yanayi na rayuwa.

Saboda haka mata kan fuskanci ciwon kai a duk lokacin da jikinsu ya samu ƙaruwa ko raguwar waɗannan ƙwayoyin halittar.

Inda ta bayar da wasu misalai na yanayi kamar haka:

  • Idan mace na yin jinin ala'ada
  • Idan tana da juna biyu
  • Lokacin da yarinya ta balaga
  • Lokacin ɗaukewar jinin al'ada, wato idan mace ta fara manyanta.

Haka kuma wasu magungunan tazarar haihuwa sukan sa wasu mata ciwon kansu ya ƙaru ko kuma ya ragu, in ji likitar.

Latsa makunnin da ke sama domin jin ƙarin bayani a cikin shirin lafiya zinariya.