Gane Mini Hanya: Tattaunawa da gwamnan jihar Kaduna 01/02/2025
Gane Mini Hanya: Tattaunawa da gwamnan jihar Kaduna 01/02/2025
A shirin na Gane Mini Hanya na wannan makon mun tattauna ne da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, kan matakan sulhu da 'yanbindiga da gwamnatinsa ke bi wajen kawo karshen matsalar kisa da satar mutane domin karbar kudin fansa.
Haka kuma Gwamnan na Kaduna ya yi bayani kan yadda ya ce yanzu ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
A baya dai jihar Kaduna ta yi fama da rikicin kabilanci da addini, a sakamakon adalcin da ya ce gwamnatinsa na yi ga dukkanin sassan jihar.