Gane Mini Hanya: Tare da shugaban hukumar samar da makamashi ta Najeriya

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Tare da shugaban hukumar samar da makamashi ta Najeriya

Hukumar kula da harkokin samar da makamashi ta Najeriya, wato Energy Commission Of Nigeria, ta yunkuro a ƙoƙarin kawo sauyi game da yadda ake sama wa al'ummar ƙasar wutar lantarki.

Har ma ta ɓullo da wasu sababbin tsare-tsare da za su inganta hanyoyin samar da wutar lantarkin, waɗanda suka haɗa da hasken rana da iska da dai sauransu.

A kan haka ne abokin aikinmu Yusuf Tijjani ya tattauna da Dokta Mustafa Abdullahi, shugaban hukumar, wanda kuma ya fara da yin bayani kan irin nauyin da ya rataya a wuyan hukumar: