Taɓa Kiɗi Taba Karatu: Yadda za ku iya yin karatu daga nesa
Taɓa Kiɗi Taba Karatu: Yadda za ku iya yin karatu daga nesa
A filinmu na Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu, mun samu baƙuncin Farfesa Aliyu Yahaya, daraktan Kwalejin Karatu daga Nesa ta Jami'ar Ahmadu Bello Zariya.
Jami'o'i a faɗin duniya ciki har da na Nijeriya kamar Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, na ci gaba da ɓullo da sabbin hanyoyin bunƙasa damar samar da ilmi mai zurfi ga ɗumbin mutanen da ke buƙatar yin haka.
Mutane masu yawa ne ke muradin zurfafa ilminsu, su samu karatun digiri amma yawan harkoki da hidimomin aiki ko sana'a, ba ya ba su dama.
Sai dai ga masu wannan buri, yanzu a iya cewa nesa ta zo kusa! Ga tattaunawar da Mukhtari Adamu Bawa ya yi da Farfesa Aliyu Yahaya.