Lafiya Zinariya: Me ya kamata ku yi don kula da lafiyar ido?
Matsalolin da suka shafi idanu na faruwa ne idan wani yanayi ya shafi yadda ido ke gani da kuma ayyukan da idon ke yi, a cewar hukumar lafiya ta duniya.
Muhimmancin kula da lafiyar ido ya sa a duk shekara aka ware ranar 10 ga watan Oktoba domin jan hankalin al'umma tare da wayar da kai kan matsalolin da ke janyo rashin gani sosai da kuma makanta.
Likitocin ido sun bayyana cewa wasu daga cikin matsalolin da suka fi damun ido, sun haɗa da Yanar ido, kuma alamominta sun ƙunshi gani dushi-dushi ko yana-yana ko farin abu a tsakiyar idanu da kuma hararagarke a tsakanin yara.
Cutar hawan jini na ido ko Glaucoma ba ya nuna alamu sai ciwon ya yi nisa, sannan ya kan kai ga makanta.
Akwai kuma matsalar gani na kusa ko nesa, wanda a kan yi gadonsa. Da matsalar raguwar gani a tsakanin mutanen da suka manyanta.
Kuma mutanen da jikinsu ba ya son wasu abubuwa wato masu Allergy a turancin ingilishi, ya kan shafi idonsu.
Babban matakin da likitoci ke cewa a ɗauka shi ne na kula da ido waje kare shi daga duk wani abu mai cutarwa, a matsayin rigakafi.
Sannan zuwa a sibiti a duk lokacin da mutum ya fuskanci wata matsala da gani ko da idonsa, don zuwa da wuri ya fi zuwa da wurwuri.