Gane Mini Hanya: Tare da shugaban hukumar daƙile kwararowar hamada ta Najeriya 16/11/2024
Gane Mini Hanya: Tare da shugaban hukumar daƙile kwararowar hamada ta Najeriya 16/11/2024
Zaizayar ƙasa da kwararowar hamada wasu tagwayen matsaloli ne da ke yin illa ga muhalli.
Wasu jihohin Najeriya na daga cikin yankin da ke buƙatar kariya game da wannan lamari.
Hukumomi a ƙasar sun kafa wata hukuma ta musamman wato 'National Agency for the Great Green Wall' don tunkarar waɗannan matsalolin, har ma da batun ɗumamar yanayi.
A filin Gane Mini Hanya na wanna makon, mun samu baƙuncin shugaban hukumar, Saleh Abubakar, wanda ya fara da bayani kan ayyukan da hukumarsa ke yi.